Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus, ya ce ba shi da niyyyar janye karar da ya shigar kotu yana kalubalantar cire shi daga shugabancin jam’iyyar da aka yi.
Mai magana da yawun Secondus, Ike Abonyi ya fada a wata sanarwa cewa, tsohon shugaban ya je kotu ne domin neman adalci da kuma kubutar da jam’iyyar daga shiga rikici.
“Hanakalin ofishin yada labarai na Secondus ya kai kan wani rahoto marar tushe da yake cewa ana matsa masa da ya janye karar da ya shigar yana mai tuhumar jam’iyyar a kotu.
“Gaskiyar maganar da labaran da ake yadawa bai fad aba ita ce, Secondus bai je koto don ya kalubalanci jam’iyya ba, sai dai an sa shi zuwa kotu ne saboda yunkurin wasu na kwace ruhin jam’iyyar.
“Saboda maganin shakku, ofishin yada labarai na sanar da cewa, tabbas Secondus na cikin yanayin neman adalci kuma zai neme shi a ko’ina saboda ya kubutar da jam’iyya daga rushewa,” in ji Ike
Ya kara da cewa jam’iyyar PDP tana sane da yanayin da ake ciki, kuma ta san abin da yakamata ta yi don magance matsalar.
“Babu wani abu na rashin adalci da zai fitar da jam’iyyar daga halin da take ciki.
“Adalcin da Secondus ke nema yana nan a cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda kuma shine kololuwa.
“Kundin tsarin jam’iyya ya bayyana karara yanda shugaban jam’iyya da ma duk wani mai mukami na kasa zai fuskanci dakatarwa a inda aka sami saba doka na bayyane ballantana kuma inda ba a karya wata doka ba.”