For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Ta Yi Watsi Da Nadin ‘Yar APC Rhoda Gumus A Matsayin Kwamishiniyar INEC

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da tabbatarwar da aka yiwa ‘yar jam’iyyar APC, Rhoda Gumus daga yankin Kudu maso Kudu a matsayin Kwamishiniyar Kasa ta Hukumar Zabe mai Zaman Kanta.

Jam’iyyar PDP ta baiyana tabbatarwar wadda ta zo bayan korafe-korafen da ‘yan Najeriya sukai a matsayin juyin mulki wa tsarin demokaradiyya, sannan kuma takalar gagarumin rikicin siyasa wanda zai ruguza demokaradiyyar da aka sha fama wajen kafawa kuma ya jawo karayar doka da oda idan har ba a gaggauta dakatar da ita ba.

Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba ne ya baiyana hakan a sanarwar da ya saki mai taken ‘Tabbatar da ‘Yar APC Rhoda Gumus a Matsayin Kwamishiniyar INEC, Juyin Mulki ne Ga Demokaradiyya.’

Jam’iyyar PDPn ta ce, “Tabbatar da Prof Gumus da Majalissar Dattawa wadda APC ke jagoranta ta yi, ya baiyana ta a matsayin marar kishin cimmuwar bukatun ‘yan Najeriya na samun ingantacce kuma sahihin zabe a shekarar 2023.

“Abun da Majalissar Dattawa wadda APC ke jagoranta ta yi, cin zarafi ne da karya doka, saboda ya saba da tanadin da ke Sakin Layi na 14 (2)(a) na sashi na 3 Kundin Tsarin Mulkin Najeriya wanda akaiwa kwaskwarima.

“Sakin layin ya ce, mamba a Hukumar Zabe zai zama marar jam’iyya kuma wanda yake da kyawawan dabi’u,” in ji PDP.

PDPn ta ce, irin wannan hawan kawara wa Kundin Tsarin Mulki da tsarin gudanar da zabe, ba zai taba sabuwa ba.

Ta kara da cewa, kafafen yada labarai a cike suke da bayanan da suke nuna cewa, Prof Gumus ‘yar jam’iyyar APC ce a jihar Bayelsa, inda take dauke da form din rijistar jam’iyya a mai lamba: BAY/YEN/08/58315, kuma aka rawaito cewa ita ce lamba ta 27 a APC wajen rijista a mazabarta.

PDPn ta kara da cewa, tabbatar da nadin dan jam’iyyar APC a matsayin mamba a INEC, ya nuna cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Majalissar Dattawan da APC ke jagoranta sun yi hawan kawarawa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 wanda sukai alkawarin yiwa biyayya.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga Shugaban Kasa da ya gaggauta janye sunan Gumus idan yana son ‘yan Najeriya su yarda da ikirarinsa na tabbatar da an yi zabe mai inganci a shekarar 2023.

Comments
Loading...