For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDP Tana Son Disashe Nasarorin Buhari, Tana Fadawa Ƴan Najeriya Labaran Ƙarya – Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a yau Litinin ya yi zargin cewa, matukar buƙatar jam’iyyar PDP na ta dawo mulki a 2023 ne ya sa take kushe kokarin gwamnatin Shugaba Buhari.

Ministan wanda ya baiyana hakan yayin da yake jawabi ga ƴan jarida a Abuja, ya ce shirin babbar jam’iyyar adawar shine ta kara rura wutar matsalar da ake ciki, ta disasar da nasarorin Buhari ta kuma yaudari ƴan Najeriya.

Ya ce, “kamar yanda kuka sani, ƴan ƙasa daga wani ɓangaren suna nan suna ƙoƙarin ruruta wutar yanayin da ake ciki, su ɓata nasarorin gwamnatinmu su kuma yada labaran da ba haka suke ba.

“Haka ne, yanayin yana yiwa mayunwata masu tsananin adawa daɗi, amma kuma

“Ta ya mutum zai fassara batunsu na kaiwa kara suna bukatar a ce taronmu ya saba doka? Ta ya zaku fassara maganarsu ta barazanar tayar da tarzomar EndSARS wadda ta fusata ƴan Najeriya? Ta ya zaku yi bayanin bayanan karya da suke yadawa game da yanayin ƙasa?

“Jama’a, babu wata matsala wajen yin adawar da ta dace a tsarin tafiyar demokaradiyya. Muna nan a baya, muka zama wadanda sukai nasara saboda a yin adawa mai kyau. Amma a lokacinmu bamu taba kira da tayar da hankalin ƙasa ba saboda kawai mun rasa yanda zamu yi.”

“Ba mu taɓa neman a bamu mulki ta hanyar hukuncin kotu ba. Idan ka ruguza ƙasar da kake son ka mulka, wacce ƙasar kuma zaka mulka? Ka yanke hancinka kuma ka ce kana so ka ɓata fuskarka?

Comments
Loading...