For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

PDPn JIGAWA: Matakin Yan Hurriyya Zubar Da Darajar Sule Lamido  Ce

Ko da yake ba wani sabon abu bane cece-kuce da wuce makadi da rawa a cikin jama’iyun siyasar Nijeriya. Sai dai babban abin tsoro shine, kadda garin tankade a watser da gari, don haka ya zama dole a na sara a dubban bakin gatari, kadda garin neman kiba a samo rama.

Kamar yadda ikirarin yan PDPn Jigawa bangaren gidan Sule Lamido suke na HURIYYA, tabbas ya dace bisa duban dabi’u da kuma gudunmawar da Dattijon ya bada wajen yantar da mutane da yawa a siyasance, wanda a haka ya taso, kuma haka yake a tarihin siyasar sa, kamar yadda na fahimta, zan dawo kan wannan batun.

Mustapha Sule Lamido da wannan tsagin suka yi gaggawar bashi takara a jama’iyar su, tabbas ya chanchanta a matsayin sa na dan jaha, mai cikekken ilimi, wanda a yanzu ya sami shekaru da dama ana damawa da shi a fagen siyasar Jihar Jigawa, harma yayi takarar Senata a Jigawa ta tsakiya a shekara ta 2019, duk da kasancewar ana ganin yana da tasgaro wajen mu’amala da mutane a siyasance da kuma kwarewa ta aiki ko jagoranci walau a gwamnati ko hukuma mai zaman kanta.

Koma dai yaya ne, zaifi kyau inda duk son nuna soyayya ko neman fada a wajen jagora don biyan bukatar yan kanzagi da sunyi amfani da hikima da kuma lokaci, ta yadda wannen hiri zai yi kyau da saurin karbuwa.

Ko kuma da sunyi amfani da daya daga cikin hadisan Jagora Malam Sule Lamido ta kauda bambanci sun bar demokaradiyya tayi hallinta, ta yadda za a bi tsari na siyasa wajen tabbatar da takara irin wannan don gudun yiwa laya mummunan rufi.

Tabbas duk dan Siyasa a Jigawa ko kana PDP ko a’a, Malam Sule Lamido Jami’a ne a siyasa, ya karantar, ya ‘yantar kuma ya hidimtawa al’ummah.

Kullum in zanyi tsokaci a siyasar Jigawa, yayin da wani abu ya sabawa tunani na, na kan tuna wata magana da Malam Sule Lamido yayi a wani taro lokacin yana gwamna, kullum ina nazarin wannan magana, kadan daga cikin abin dana fahimta shine “….munyi gwagwarmaya, an kama mu, an daure mu a baya, don ganin talaka ya samu yanci, ya samu damar damawa da shi a mulkin kasar sa, ….. a yau duk inda ka leka, in kaje office din kwamashina, ko Permanent Secrectary, ko adviser ….. za ka ga mafi yawa yayan talakawa ne a ciki………….” Amma fa a yau shi talakan ne ke gallazawa kansa tun daga damar samun yanci da kuma yin siyasar.

A takaice yau talakan da ba kowa ba a baya, siyasa ta mai dashi wani, ya zama Chairman na Karamar Hukuma ko Kwamashina, minister, SA, PA ko ya zamo sananne shike kokarin maida hannun agogo baya, bayan an sami yancin huriyya a ke kokarin dawowa da mulikiyya ta hanyar ganganci da maganar bakan da ba ta kai zuci ba.

Tabbas, a zahirance kamar yadda na fada, aiyukan Sule Lamido a siyasa ya nuna shi cikekken dan kasa ne mai kishin kasar sa da yankin sa.
Domin ya zagulo duk wani mai basira ko ilimi da zai taimaka wajen ciyar da Nijeriya ko Jihar Jigawa gaba, ya fito da daukakak da yawa kuma har yau yana yi, ba don nasaba ba ko bangarenci, wasu a cikin su ba kawai sun nuna kansu a Nijeriya da duniya bane, sun daga darajar Jigawa ne da kuma nuna muhimmancin shi kansa Malam Sule Lamidon wajen kwarewa a cikin gwagarmaya da zagulo masu baiwa daga tarun mutane.

Irin wadanna mutanen suna nan birjik a fadin kasar nan da ma Jihar Jigawa, Sule Lamido ne yayi sanadiyar sanin mutane kamar Ahmed Abdulhamid Malam madori tsohon minsitan wutar lantarki kuma tsohon ambassador, Professor Rukayya, tsohuwar ministan ilimi ta tarayyar Nijeriya, Ambassador Kazaure tsohon minister kuma tsohon shugaban PDP na Arewa-maso-Yamma, Hajiya Hauwa Bello tshohuwar Ministan Niger Delta, Malam Yakubu A. H Ruba  (SAN) tsohon kwamishinan Shari’a, marigayi Professor Haruna Wakili, Dr. Nuruddeen Muhammad tsohon ministan Harkokin Kasashen Wajen, Malam Salisu Mamuda Ku’it tsohon shugaban Jama’iyyar PDP na Jihar Jigawa da sauransu duk kannin su a nawa binciken alakar su da Malam Sule Lamido siyasa ce, kuma jagorancin sa ne ya sa aka ma san wasu da ga cikin su. Wannan kadai ba karamin karatu bane a wurin Jagora Sule Lamido.

Amma, yau a ce a wannan gabar tunanin Sule Lamido ya koma a gaje shi, a neman tarwatsa darajar muhimin mutun a siyasar Nijeriya ne, sannan kuma kara gishiri ne a kan gyambon da ake neman warkewar sa. Duk wanda ya san waye Sule Lamido zai yi wahala ya yarda cewa siyasar sa zata kare ta irin wanna salo da ya sabawa zamanta kewar siyasa na yanci da huriyya.

Muna nan muna sauraro

Ahmed Ilallah
alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...