For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Peter Obi Ya Taya ‘Babban Yaya’ Atiku Abubakar Murnar Cika Shekara 76 A Duniya

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a jiya Juma’a ya taya abokin hamayyarsa a zaben shekarar 2023, Atiku Abubakar murna cika shekara 76 a duniya.

Atiku Abubakar dai shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023 mai zuwa.

A wani jawabi da ya saki, Peter Obi ya ce, “Cikin nuna soyayya Babban Yaya, Mai Girma Alhaji Atiku Abubakar, ina taya ka murna a daidai lokacin da ka cika shekara 76 a duniya a yau.”

“Ina fatan Allah da yai maka wannan baiwa ta tsawon rayuwa, ya kare ka sannan ya kuma yi maka albarka a ko da yaushe. Ina taya ka murna.”

Peter Obi dai shine wanda yai wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Comments
Loading...