Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya zama dan takarar Shugaban Kasa na jamíyyar Labour Party domin tunkarar babban zabe na shekarar 2023.
Nasarar ta sa ta biyo bayan samun nasarar da yai a zaben fidda gwani na jam’iyyar Labour Party wanda aka gudanar yau Litinin a Asaba ta Jihar Delta.
Wakilai guda 185 ne aka tantance domin yin zaben, wadanda zasu zabi mutum 1 cikin mutane 4 da ke neman tsayawa jam’iyyar takarar Shugaban Kasa.
Sai dai kuma duk sauran ‘yan takarkarun guda uku wadanda suka hada da Farfesa Pat Utomi, Olubusola Emmanuel-Tella, da Faduri Joseph sun janyewa Peter Obi kafin a fara zaben.
Tsohon gwamnan ya samu nasarar yiwa Labour Party takarar ne kimanin sati daya da sanarwarsa ta ficewa daga jam’iyyar PDP tare da janyewa daga neman takarar shugabancin kasar a karkashin tsohuwar jam’iyyar ta sa.
Kwanaki uku bayan barin tsohuwar jam’iyyar tasa ta PDP, Peter Obi ya shiga jam’iyyar Labour Party domin cimma burinsa na samun gadon kujerar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a 2023.