Daga: Muhd Yobe
Plateau United karkashin jagorancin mai horarwar ta Abdu Maikaba tana ci gaba da yunkuri domin sake lashe gasar NPFL ta Najeriya, hakan ne yasa taci gaba da yin garambawul a Kungiyyar.
Kafin hakan dai kungiyar ita ce ta lashe gasar Firimiyyar Nijeriya a 2020 wacca ana cikin bugawa aka dakatar saboda bullar cutar Corona, daga bisani bayan hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF da kamfanin dake shirya gasar firimiyyar Nijeriya LMC sun tattauna suka yanke shawarar cewa Plateau United ce ta lashe gasar.
Amma a gasar da aka kammala ta kwana nan ta 2021 Plateau United ta kasa rike kambunta, inda ta kammala gasar a mataki na 9 da maki 51.
Kawo yanzu dai Kungiyyar ta samu nasarar sayen wadannan ƴan wasan.
- Jimmy Ambrose daga Wikki Tourist
- Nwani Ikechukwu Morgan daga Akwa United
- Uchegu Emmanuel daga Ifeanyi Una
- Chimeze Izuchukwu Victor daga MFM FC
- Reuben Bala daga Enyimba
- Muh’d Muh’d Umar daga GBS
- Muhammad Abubakar daga GBS
- Olakunle Akala daga GBS
- Dennis Victor daga Kano Pillars
- Oyaleso Suraj daga Kano Pillars
- Babaginda Abubakar daga Rarara FC
- Alex Aghahowa daga Lobi Stars
- Samuel Mathias daga Lobi Stars
- Oguacha Eric Epere daga ifeanyi Una
- Haggai Katoh daga Nassarawa United
- Reuben Nicodemus daga Nassarawa United
- Oghene Elijah daga Katrina United