Duba da ka’idojin tabbatar da kafuwar sabuwar makaranta, Gwamnatin Tarayya ta sanar da nadin jagorori (principal officers) na sabuwar Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya (Federal University of Technology) da ta samar Babura, Jihar Jigawa.
Ma’aikatar Ilimi ta kasa ce ta sanar da nadin ne a wata sanarwa da ta gabatar ga manema labarai a jiya Talata a Abuja ta hannun Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar, Mr Ben Goong.
Farfesa Sabo Ibrahim, kwararre a fannin ilimin wutar lantarki, shine gwamnatin ta nada a matsayin Shugaban Jami’ar ta FUT Babura.
Kafin nadin nasa, Farfesa Sabo malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano (Bayero University, Kano), haka kuma ya wallafa takardu da dama a fannin ilimin fasahar lantarki da cigaban ilimi a mujallu na cikin kasa da kuma na duniya.
Farfesa Sabo dan Jihar Jigawa ne, jihar da jami’ar ke ciki, ya fito ne daga Karamar Hukumar Birnin Kudu da ke jihar.
Sanarwar nadin Farfesa Sabo Ibrahim a matsayin Shugaban Jami’ar Federal University of Technology, Babura ta kuma baiyana sunan Fatima Mohammed a matsayin Rigistrar, Ibrahim Alhassan a matsayin Bursar, da kuma Abashe Atiku a matsayin Librarian.
Sanarwar ta kuma baiyana cewa, an yi wadannan nade-naden ne domin a gaggauta fara gudanar da jami’ar.
Idan za a iya tunawa, a shekarar 2021 ne dai, Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya, NAN ya rawaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta kirkiro da sabbin jami’o’i guda hudu ciki har da FUT Babura, domin magance matsalar karancin ilimin kimiyyya da fasaha, ilimin likitanci da kuma ilimin sanin sinadaran kara lafiya.
NAN din ta rawaito cewa, Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya ce, Shugaban Kasa ya amince da fitar da kudaden fara gudanar da jami’o’in, inda aka warewa jami’o’i biyu na fasaha naira biliyan 4 kowaccensu daga asusun Tertiary Education Trust Fund (TETFund).