For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Qatar Na Neman Karbar Baƙuncin Gasar Olympic Ta 2036

Kwamitin kula da harkokin gasar motsa jiki ta Olympics na Qatar ya sanar da aniyar gwamantin ƙasar na karɓar baƙuncin gasar wasannin motsa jiki na 2036.

BBH Hausa ya rawaito cewa, kwamitin ya tabbar da cewar Qatar ta miƙa bukatar karɓar baƙuncin karon farko don amincewa, ga kwamitin shirya gasar wasanni motsa jikin ta duniya, wanda hakan ba zai hana a bincika tare da duba yiwuwar ko tana da damar da zata karɓi irin wannan gasa.

Sanarwar dai na ƙunshe a wani sako da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Suma kasashen Indonesia da Inidiya sun nuna sha’awarsu na karbar baƙuncin gasar ta Olympics.

Qatar ta yi hasashen samun kuɗin shiga da ya kai dala biliyan 20 a gasar cin kofin duniya na 2022 da aka kammala a baya-bayan nan, wanda hakan ya sa ƙasar, take son karbar bakuncin gasar, saboda irin tsarin filiayen da take da su.

A baya a shekarun 2016, da 2020 da 2032 an ki amincewa da buƙatar Qatar na karɓar baƙuncin gasar wasannin na motsa jiki.

Comments
Loading...