A yau Lahadi ne wakilan Jamiyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, reshen mazaɓar Majalissar Dattawa ta Arewa maso Yammacin Jihar Jigawa suka zaɓi Rabi’u Isah Taura a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar takara a babban zaɓe na shekarar 2023.
Rabi’u Taura dai ya kasance ɗan takara ɗaya tilo da ke neman wannan kujera, saboda haka an buƙaci amincewar wakilan ne a tare, inda duk suka amince da murya guda.
Zaɓen ya samu shedawar wakilan Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da sauran magoya bayan jam’iyyar NNPP na mazaɓar.
Rabi’u Isah Taura ya taɓa zama Sakataren Jam’iyyar ANPP na Jihar Jigawa, sannan kuma ya zama Sakataren Jam’iyyar PDP na Jihar.
Rabi’u Taura, ya yi Kwamanshinan Ma’aikatar Noma da Alabarkatun Ƙasa ta Jihar Jigawa.
Kafin samun wannan matsayi, shine Shugaban Jam’iyyar NNPP na Arewa maso Yammacin Jihar Jigawa.
A yanzu dai Rabi’u Isah Taura zai kara neman Ɗan Majalissar Dattawa ne tare da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Ibrahim Saminu Turaki daga PDP da kuma Babangida Hussaini Kazaure daga APC.