For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Rasha Ta Gargaɗi Ecowas Kan Tura Sojoji Nijar

Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar Ecowas game da ɗaukar matakin soji da ta ce za ta yi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Tana mai cewa matakin ka iya haifar da rikicin da zai daɗe ba a ga ƙarshensa ba.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar ranar Juma’a ta gargaɗi ƙasashen yammacin Afirka da kada su aika sojoji zuwa Nijar.

Sanarwar ta ce ”Mun yi imanin cewa matakin soji ba zai warware matsalar Nijar ba, a maimakon haka lamarin zai haifar da mummunan rikici, wanda ba a san ranar ƙarewarsa ba, tare da sake dagula lamura a yankin Sahel”.

Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas na shirin wata ganawa a ranar Asabar domin tsara yadda za a shirya dakarun sojin.

KARANTA WANNAN: Amurka Ta Ce In Aka Takura Mata Zata Mamayi Nijar

A ranar Juma’a ne ƙungiyar Ecowas ta amince da kafa ‘rundunar ko-ta-kwana’ a shirye-shiryen ɗaukar matakin soji kan sojojin na Nijar.

Tuni dai shugaban ƙasar Ivory Coas, Alassane Ouattara, ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.

Ƙasashen Amurka da Faransa da kuma Tarayyar Turai tuni suka goyi bayan matakin da ƙungiyar Ecowas ta ɗauka, domin mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

A ranar Juma’a magoya bayan sojojin na Nijar riƙe da tutar ƙasar Rasha sun gudanar da zanga-zanga a harabar ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai.

Inda suka riƙa kiran ƙasashen yamma su fice daga ƙasar tare da kira ga Rasha ta kawo musu ɗauki.

Rasha dai ba ta fito ƙarara ta goyi bayan juyin mulkin na Nijar ba.

Ƙasashen Faransa da Amurka na da sansanonin soji a Nijar, domin yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

BBC HAUSA

Comments
Loading...