Shugaba Putin ya ce yana son su zauna gaba da gaba da takwaransa na Ukraine a yarjejeniyar.
Turkiyya ta bayyana sharuddan da Rasha ta gindaya domin kawo karshen yakin da ta kaddamar na mamayar Ukraine, inda wasu ke da sauki wasu kuma masu wuya ne ga makwabciyar tata.
Wannan ya biyo bayan tattaunawar da aka yi ne ta waya tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Rasha Vladamir Putin.
Cikin sharaddun har da cewa lallai ne Ukraine ta kasance kasa ‘yar baruwanmu a nan gaba kuma ta daina duk wani buri na shiga kungiyar tsaro ta Nato.
Bisa ga dukkan matsayin da Turkiyya ta dauka na shiga tsakani a wannan yaki na Rasha da Ukraine kwalliya na biyan kudin sabulu.
A ranar Alhamis da yamma ne dai Shugaba Vladimir Putin ya buga wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan, a matsayin mai neman maslaha a rikicin, inda ya bayyana wa takwaran nasa ainahin abubuwan da Rasha ke son ganin sun tabbata idan har ana son zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
Bukatun na Rasha dai sun kasu gida biyu, inda jerin hudu na farko wadanda ba masu wuya ba ne ga Ukraine ta cimma suka hada da cewa Ukrine ta zama kasa ‘yar baruwanmu a lamarin da ya dangnaci kasashen Yamma da Rasha, kuma kada ta taba zama ‘yar kungiyar NATO, wanda tuni daman Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky ya bayar da kai a kan wannan.
Sauran na wannan rukuni na farko su ne cewa dole ne Ukraine ta rabu da makaman da za ta daina zama barazana ga Rasha
Sannan wajibi ne a tabbatar da kare harshen Rasha a kasar ta Ukraine, da kuma abin da Rashar ta kira rabuwa da akidar ‘yan Nazi.
To amma kuma wannan sharadin da Rasha ta kira akidar ‘yan Nazi, abu ne tamkar na cin fuska ga Shugaba Zelensky, wanda shi kansa Bayahude ne, da kuma dangin wasu da aka kashe a lokacin kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa.
Sai dai duk da haka Turkiyya na ganin abu ne mai sauki Shugaba Zelensky ya amince da hakan.
Domin watakila Ukraine ta fito fili ta soki duk wani salo na akidar da Rashar ke gani ta ‘yan Nazi, bugu da kari ta ma shiga kama masu wannan manufa.
Sai kuma kashi na biyu na bukatun na Rasha inda ake ganin nan ne matsala za ta iya kasancewa.
Na farko shi ne Shugaba Putin ya ce yana son tattaunawa ta gaba da gaba tsakaninsa da takwaransa na Ukraine din Mista Zelensky, kafin a cimma duk wata yarjejeniya, kuma daman wannan abu ne da Zelensky ya ce a shirye yake.
Sai kuma batun matsayin Donbas, a gabashin Ukraine, wanda yanki ne da wani sashe nasa tuni ya ware daga Ukraine, tare kuma da jaddada kasancewarsa na Rasha, sannan kuma da matsayin Crimea.
Abin da wannan ke nufi a takaice shi ne Ukraine ta hakura da wannan yanki na gabashinta, wanda wannan abu ne mai wuya a wurinta.
Hakan dai na nufin Rasha na bukatar Ukraine ta fito ta tabbatar a hukumance cewa ta amince Crimea wadda Rasha ta mamaye a 2014, mallakar Rashar ce a yanzu.
Ana ganin cewa idan har ba a yi da gaske ba kuma cikin tsanaki wajen fayyace wadannan sharuda da Rasha ta gabatar, nan gaba Shugaba Putin ko duk wani da zai gaje shi, zai yi amfani da su a matsayin dalilin sake mamayar Ukraine.
Haka kuma ana ganin yarjejeniyar zaman lafiya ka iya daukar dogon lokaci kafin ta tabbata, ko da kuwa an dakatar da zubar da jinin da ake yi a yanzu
Ukraine dai ta tafka asara a wannan yaki a cikin ‘yan makonnin da suka gabata, kuma sake gina garuruwa da biranen da Rasha ta barnata zai dauki lokaci mai tsawo.
Haka kuma sake samar da mazauni ga miliyoyin ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga gidajensu.
(BBC Hausa)