Kasar Ukraine ta ce tara daga cikin cibiyoyin samar da wutar lantarkinta sun lalace a wasu manyan sabbin hare-haren makamai masu linzami na Rasha, kuma yawan makamashin da ake amfani da shi a kasar ya ragu da fiye da rabi.
An rawaito cewa, hare-haren da aka ce sun kai akalla sittin, sun kashe akalla fararen hula uku a tsakiya da kuma kudancin Ukraine, haka kuma a birni na biyu mafi girma a kasar wato Kharkiv, babu wutar lantarki.
Rahotanni sun ce ana cikin yanayi mai wahala a Kyiv inda kankara ke zuba, abin da ya sa mutane a nan da sauran garuruwa ke cikin mawuyacin hali.
Ana fargabar baraguzai sun danne wasu, yayin da wani makami mai linzami ya dira a wata majalissa da mutane ke hutawa a birnin Kryvyi Rih da ke tsakiyar kasar.
BBC Hausa