For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Rashin Baiwa Mata Muhimmanci Da APC Ke Yi Shi Zai Kayarta A Zabe – Mariya Waziri

An bayyana mata a matsayin mafiya rinjaye wajen zabar shugabanni a bangarorin daban-daban na siyasa, to sai dai amma ba a damawa da su yanda ya kamata.

Hajiya Mariya Waziri, Shugabar Kwamitin PRACO da ke karakashin Hajiya Rukayya Atiku Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ce ta bayyana hakan a babban taron mata na shiyyar Arewa maso Yamma.

An gabatar da taron ne ranar Juma’ar da gabata, 4 ga watan Nuwamba, 2022 a birnin Kano.

Mariya Waziri ta ce, “Kamar yadda yake a kunshe a cikin manufofin Atiku Abubakar da ya gabatar kwanan nan ya ce, mata ne kaso 50% na adadin mutanen Najeriya amma basu da ƙarfin tattalin arziki, ba a damawa da su a siyasa, al’amura, al’adu da kuma tattalin arziki a cikin gida da waje”.

“Abun farin cikine yanda wannan kwamatin na PRACO ƙarƙashin mai dakin shugaban ƙasa mai jiran gado Hajiya Rukayya Atiku Abubakar ya hadamu waje ɗaya a matsayin ‘yan uwa, domin mu tattauna mu samar da mafita a kan hanyoyin da za a bi wajen damawa da mata a siyasa.”

Mariya Waziri ta kara da cewa, Atiku Abubakar ya bayar da dama ga mata da su tattauna a junansu kan yanda suke so a dama da su a gwamnatinsa, haka kuma mata zasu iya samu kaso 35 na mukamai a gwamnatin Atiku kamar dai yanda tsarin Majalissar Dinkin Duniya ya bukata.

“Wannan ya yi daidai da tsarin samar da daidaito tsakanin kowanne jinsi wanda aka tsara bawa mata kaso 35% a dukkan tsarukan tafiyar da gwamnati. Shin ana bawa mata kaso 35%? Shin zamu samu kaso 35% a gwamnatin Atiku? Tabbas zaku ji daɗi a gwamnatin Atiku Abubakar domin zai bawa mata dukkan damar da ya kamata.”

“Ƙarancin yanda APC ta ki ta dama da mata, shi kaɗai zai sa su fadi zabe kuma Atiku zai yi nasara a 2023 domin shi kadai ne ɗan takarar da a Najeriya yake da tanade-tanaden a kan mata a siyasar Ƙasar nan,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga dukkan mata na shiyyar Arewa maso Yamma da su zabi Atiku Abubakar a zaben shekarar 2023, tare da jawo kan ‘ya’yansu da mazajensu wajen ganin Atiku ya kai ga nasara a zaben, abun ta bayyana a matsayin abun da zai kawo ci gaba ga dukkan mata.

Ta kuma ce, “Atiku ya shirya sharewa mata hawayensu a kan halin da suke ciki na rashin basu dama. Atiku ya samar da tsare-tsaren da zasu tabbatar mata, matasa da tsofaffi ana damawa dasu dan gina ƙasar nan, amma, ba zamu amfani wannan ƙudurorin ba har sai mun yi fitar ɗango mun zaɓi Atiku a 2023.

Cikin manyan baki da suka halarci taron akwai Hajiya Rukayya Atiku Abubakar, Hajiya Amina Namadi Sambo, Hajiya Hauwa Musa Kida da kuma sauran shugabannin mata na shiyyar Arewa maso Yamma.

Comments
Loading...