For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Rigimar Gwamna Badaru Da Tsohon Shugaban APCn Jigawa Sara Da Jahun Barazana Ce Ga Yancin Dimokaradiyya

Daga: Ahmad Ilallah

Kullum abin takaici a irin siyasa ta Jigawa, shine rashin hakuri, fahimtar juna tsakanin jagorori da mabiyan su. Uwa uba, daukan bangaren munafurcin siyasa yayi tasiri a kan zahirin gaskiya. Wanda a karshe ba wanda zai ga da kyau.

Shifa mulki da jagorancin siyasa,  tamkar daukan jinka ne,  mutu guda bai isa dauka ba, sai an taru, kamar yadda a taru a kafa Jama’iyar har a ka kaita ga nasara.

Abin mamaki ne da takaici, a ce anyi  zama na shekara takwas babu wata guda tsakanin wannan mutanen da gwamna Badaru, wani lokacin ma sune yan lelan sa, amma a ce a kasa da wata guda an samu mummunan karshe, har ta kai ga dauri da gurfanar wa gaban Kuliya.

Habibu Sara tsohon shugaban Jama’iyar APC ne na Jihar Jigawa,  wanda kafin haka shine Mataimakin Jama’iyar APC na Farko, ya zamanto Shugaba bayan tsohon shugaban Jama’iyar an zabe shi wakili a majalissar dokoki ta kasa. Shi kuma Malam Karami Jahun sannan Dan Sojan Bakan Jama’iyar APC ne.

Shin menene ya zafi, har a ka kai wannan yanayi, na tsare wannan mutane da gurfanar da su a gaban Kuliya?

Duk da ance zargin da Gwamnatin take yiwa wadannan mutane, shine batun da suka yi a radio na zargin da suka yiwa Gwamnati Badaru mai shirin barin gado daban, daban, shi ya jawo wannan rigima, har ya fusata Gwamnatin daukan wannan mataki.

Amma fa, Hausawa sunce, shi maigaskiya baya fada, ya kamata Gwamnatin ta fito ta karyata batutuwan su,  da kuma yiwa mutane Jigawa gamsashen bayani a kan batun, ba sai an kai ga wannan danbarwa ba.

Ya kamata musani fa,  babbar ribar dimokaradiyya shine sanya baki da yadda a ke mulkin ka, tsokakaci da fadar gaskiya a kan yadda a ke jagorancin alumma.

Tauyewe mutane damar yin magana a kan harkar gwamnati ta irin wannan hanyar, ko yin barazana, tamkar yiwa dimokaradiyya ne zagon kasa.

Duk da cewar, ba kawai mai mulki ba, hatta talaka ba zai so ayi masa mummunan zargin da zai zubda masa daraja ba. 

Amma fa musani,  duk wanda Allah ya bashi damar mulkin mutane bai kaucewa irin wannan batutuwan,  gaskiyar sa ce kadai mai fidda shi.

Muna rokon mai girma gwamna, da ya du ba wannan batu da kuma yin hakuri akai, domin tamkar rigima ce tasu ta cikin gida, a samu maslaha a gida.

Zai zamanto kuskure mafi girma kuma abin kwatance a irin wannan lokaci na yafar juna, a ce an kare a irin wannan matsayi, tsakanin ka da wadannan yaya naka.

Lokaci ne ga duk wani mai kaunar Badaru, zai so Badaru yayi sallama da kowa lafiya.

Ahmed Ilallah ya rubuto ne daga Hadejia, Jigawa

alhajilallah@gmail.com

Comments
Loading...