Daga: BBC Hausa
Gwamnatin Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta musanta jita-jitar da ke yawo cewar gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PRP.
Jita-jitar ta biyo bayan ganawar da ɓangaren APC na gwamnan ke yi a ƙoƙarin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata kotu ta yi a Abuja game da zaben shugabanin jam’iyyar a mazabu da kananan hukumomin Kano.
Hukuncin kotun na ranar Juma’a ya ba ɓangaren Shekarau da ke rikici da ɓangaren gwamna Ganduje nasara.
Alƙalin kotun mai shari’a Hamza Muazu wanda ya zartar da hukuncin ya kuma buƙaci ɓangaren gwamna Ganduje da ke neman a yi watsi da shugabancin ɓangaren Shekarau ya biya tarar miliyan ɗaya.
An danganta shirin gwamnan na sauya sheka daga jam’iyyar ta APC sakamakon hukuncin wanda ya ƙara zafafa rikicin APC a Kano tsakanin ɓangaren gwamnan nda na tsohon gwamna Sanata Shekarau.
Sai dai cikin wata zantawa da BBC Hausa, kwamishinan raya karkara na jihar Musa Iliyasu Kwankwaso, wanda yana ɗaya daga cikin jiga-jigan ɓangaren na Ganduje, ya ce batun ba shi da wani tushe ballantana makama.
“Sune suke ƙoƙarin ficewa daga APC ba mu ba, amma gwamna wanda yake kan kujera ya zai yi haka, an ma kawo gwamnan da ba a jam’iyya yake ba kuma da ya shigo ya karbi jagorancin jam’iyya, sannan kuma a ce gwamnan da ke cikin jam’iyyar zai fice saboda rikici, sune suke shirin ficewa” a cewarsa.
Ya kara da cewa ”Jam’iyyar APC ta mu ce, kuma za a ci gaba da kokarin yin sulhu, domin rikicin siyasa ba sabon abu ba ne kuma za a zo a daidaita idan har wadanda ke rikicin da su na nan cikin jam’iyyar ba su fita ba”
Wani abu da ke sake fito da rikicin ƙarara shi ne rushe zabukan shugabannin mazabu na jam’iyyar wanda bangaren gwamnatin jihar ta gudanar da kotu ta yi, bayan shigar da kara da bangaren Malam Ibrahim Shekarau ya yi.
‘Za Mu Ɗaukaka Ƙara’
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce za su ɗaukaka kara a kan hukuncin, wanda babbar kotun da ke Abuja ta yanke, kuma ta ƙara jaddada shi.
A cewarsa ”Akwai kotu ta gaba ta daukaka kara, kuma za mu daukaka, muna sa ran za a yi mana adalci a warware wannan hukunci, don a baya ma ba a duba hujjujojin da muka kawo ba aka yanke hukunci,
”Babu maganar Danzago kwata kwata a shugabancin APC a Kano, domin ai ba da ka ake shugabancin jam’iyya ba, ba al’amari ne na wasa ba, su da suke da’awar shugabanci ai ba su yi zaɓen ba, kuma babu wanda ya turo musu jami’ai daga shalkwatar jam’iyya ta kasa” inji shi.
Rikicin da ke tsakanin ɓangaren Ganduje da na Shekarau a Kano ya yi sanadin rabuwar jam’iyyar gida biyu inda Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar ɓangaren Shekarau sai kuma Abdullahi Abbas ɓangaren Ganduje.
Wasu na ganin rabuwar kan APC a Kano wata babbar ɓaraka ce ga jam’iyyar a Najeriya musamman yanzu da ake tunkarar zaɓen 2023.