Kwanaki bayan dakatar da tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da shugabancin jam’iyyar APC na mazabarsa ya yi saboda zarginsa da aiyukan yiwa jam’iyya zagon kasa, shugabancin jam’iyyar na jiha ya soke dakatarwar.
A wata wasika ta dakatarwa da shugaban APC, Sa’idu Laminu Baban Karatu da sakataren APC, Abdullahi, dukkaninsu na mazabar Makama/Sarkin Baki da ke Karamar Hukumar Bauchi suka sanyawa hannu, sun ce dakatar da tsohon gwamnan ya zo daidai da tanadin doka mai lamba 21(2) na kundin tsarin mulkin APC.
KARANTA: Sau 50 Aka Kai Hare-Hare A Ofisoshin INEC Daga Shekarar 2019 Zuwa Yanzu
To sai dai kuma, a wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na APC reshen jiha, Adamu Aliyu Jallah ya sanyawa hannu, ya bayyana dakatarwar a matsayin haramtacciya wanda ba ta kan ka’ida.
Sanarwar ta Jallah, ta soke korar da aka yiwa tsohon gwamnan da taken ‘Soke Haramtacciyar Korar da Aka Yiwa Mai Girma Mohammed.’
Takaradar ta ci gaba da cewa, “Kirkirarren hukuncin da ke cikin takardar dakatarwa mai kwanan wata 14/12/2022 yan zama sokakke kuma abin watsi ga shugabancin jam’iyyar APC na Jihar Bauchi, saboda gaza bayar da dama da kuma sabawa tsarin ladabtarwa da ke magana ta 21 a kundin tsarin APC na shekarar 2022.
“Saboda haka a kula, Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN, har yanzu shi dan jam’iyyar APC ne, kuma zai ci gaba da kasancewa a cikin aiyukan jam’iyya a matakai daban-daban, har zuwa sanarwa ta gaba.”
Tsohon Gwamnan dai ya fada cikin zargi ne a makon jiya, bayan ya ziyarci taron cin abincin da Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya shirya masa a matsayin taya shi murnar hawa mukamin Babban Lauyan Najeriya wato SAN.
An rawaito cewa, Mohammed ya yabawa gwamnan a wajen cin abincin, inda ya ce, “Dole ne na yabawa kanina bisa gagarumar nasarar da ya samu a bangarori da dama na tattalin arzikin jiha.”