For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Rikici Ya Tilasata Wa Dubban ‘Yan Sudan Ta Kudu Guduwa Sudan

A kalla mutane 1,700 ne suka tsere wa rikicin da ke faruwa tsakanin bangaren sojoji a arewacin Sudan Ta Kudu kusa da kogin Nile wanda ya gangaro cikin Sudan, kamar yadda gidan jaridar Sudan din Suna ya rawaito.

Hukumar Unicef, ta ce rikici tsakanin sojojin da ya fara a watan Agusta ya tilastwa dubban maza da mata tserewa daga muhallansu, saboda ci gaba da samun kashe fararen hula da ake yi, ana sace wasu sannan kuma a raunata wasu, abun da ya sa rikicin ya watsu zuwa yankin Jonglei da na Unity.

A ranar Laraba, Majalisar Dinkin Duniya ta ce, rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane 166 ya zuwa yanzu, a daidai lokacin da ake ta kiraye-kiraye ga kungiyoyin ba da agaji su kai agajin gaggawa ga wadanda suke neman tsira.

BBC Hausa

Comments
Loading...