Wasu fusatattun dangin Mai Martaba Sarkin Dutse, Hamim Nuhu Sunusi, sun kutsa gidan kwanansa, inda su ka ci zarafin fadawa tare da sara abokin sarkin na ƙuruciya bisa kalaman da aka yi kan kawun sarkin, Galadiman Dutse, Basiru Sunusi.
Wata majiya daga Fadar Sarkin ta shaidawa wakilin jaridar 247UREPORTS cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:20 na tsakar dare, yayin da Sarkin ya kwanta domin yin bacci a gidansa.
KARANTA WANNAN: Dubunnan Mutanen Da Suka Mutu A Dalilin Faɗan Manoma Da Makiyaya
Majiyar ta ce, ƴaƴan Galadiman Dutse na zargin Sallaman Sarkin Dutse, Yaya Muhammad da faɗin baƙaƙen maganganu a kan Galadiman wanda kawu ne a wajen Sarkin, inda kuma suke zargin Sarkin da ɗaure masa gindi.
Jaridar ta rawaito cewar, lokacin da ta tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya musanta faruwar lamarin, inda ya ce, idan ya tabbatar da gaskiyar batun zai tuntuɓi jaridar.