Dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a jamiyyar PDP a zabukan 2015 da 2019, Aminu Ibrahim Ringim ya bayyana cewa suna zargin tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da hadin baki da jamiyyar APC abin da yai zargin ya jawo rashin nasarar PDP a zabukan 2015 da 2019 a jihar.
Aminu Ibrahim Ringim ya baiyana hakan ne a wata hirar da yai da BBC Hausa, a tattaunawar da akai kan batun da Sule Lamido ya tattauna da BBC a kai kafin wannan.
Tunda farko dai Sule Lamido ya bukaci Aminu Ringim da ya fito ya baiyana laifin da ya yi masa, inda shi kuma zai same shi har gida ya ba shi hakuri.
Sai dai a cikin bayanan Aminu Ringim ya baiyana cewa ba bayar da hakuri ne mafita kan matsalar ba, face jam’iyyar PDP ta Kasa ta zo ta yi abinda ya dace dangane da shugabancin jam’iyyar PDPn reshen jihar Jigawa matukar dai tana fatan kaiwa bantenta a zaben 2023.
A ganin Aminu Ringim mafita kan wannan rikici nasa da Sule Lamido ita ce, “Jam’iyyar PDP tai adalci, tai shugabanci. Yanzu in ka zo ka ce ba ma neman biyayya, mun yi shekara daya da rabi babu shugabanci a jam’iyyar, ba ma ciki, ba a yin komai da mu, ba abin da akai da mu. Jam’iyyar nan mun yi kuka ne kan cewa a yi zabe, in an ka da mu, mun yarda. Shi ya tashi ya ce, ba za ai zabe ba, duk jihar Jigawa sun san jam’iyyar PDP ba a yi zabe a cikinta ba. Amma muka tafi muka zo aka daure, muka daure akai kara a kotu, aka ce huldar jam’iyya ce, muka tafi appeal court, aka ce huldar jam’iyya ce, yanzu mun tafi supreme court. Abin da muke jira jam’iyya a ce ita ce ko ita ce ko ba ita ba ce, sannan sai mu ga matakin da zamu dauka.
A karshe an tambayi Aminu Ringim kan cewa ko za su hakura su hade domin a samu nasara tare, inda ya ce, “Shine daidai, shine daidai in za a hade din, to amma babba ne me hadawar, ko ba ya ce shine babba ba, ya ce shi ba sa’a na ba ne, . . . kuma na yarda, amma dai babba mai adalci shine yake fin kowa, babba mai yin daidai shine mai yin kowa, babban da ba ya son zuciya shine mai yin kowa – wannan shine amsar.”