Rudani ya barke a zaman manyan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, wanda aka gudanar ranar Litinin da daddare, bisa kokarin tilasta Shugaban Jam’iyyar Nakasa, Iyorchia Ayu na canza lokacin zaman zuwa yau Laraba.
Rudanin dai ya faru ne dalilin bukatar wasu jagorori daga yankin Kudu, wadanda suka nemi cewa dukkan wadanda suka koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC a baya, sannan suka dawo jam’iyyar kar a basu damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Wani gwamna mai yawan Magana daga yankin Kudu ne ya jagoranci kiran, kamar yanda majiyar ta nuna.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki; tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal na daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka koma jam’iyyar APC a lokacin neman babban zaben shekarar 2015.
Bayan haka kuma, dukkaninsu sun dawo jam’iyyar PDP biyo bayan sabanin da ya kasa daidaituwa tsakaninsu da gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC.
Wasu daga cikin wadanda suka koma jam’iyyar PDPn sun ci zabe a jam’iyyar a zaben 2019 yayin da wasu kuma suka fadi, duk karkashin tutar jam’iyyar PDPn.
Dukkaninsu, suna neman samun damar jam’iyyar domin yi mata takara a zaben shugaban kas ana shekarar 2023.
Wadanda ke rura wutar neman ware wadanda suka bar jam’iyyar a baya, sun baiyan cewa, komawarsu APC ce ummul-aba’isin faduwar jam’iyyar PDP a shekarar 2015.
Sun kara da cewa, wadannan mutane sune suka sanya jam’iyyar PDP kasancewa jam’iyyar adawa a Najeriya.
‘Yan jam’iyyar daga yankin kudu, wadanda aka kuma rawaito cewar suna kiran da a mika wa yankin kudu takarar shugaban kasa a jam’iyyar, sun baiyana cewa, rashin mutunta yarjejjeniyar karba-karba a jam’iyyar daga bangaren tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ce ta jawo yoyewar ‘yan jam’iyyar a zaben shekarar 2015.
To sai dai kuma, wasu ‘yan jam’iyyar daga yankin arewa, sun musanta kiraye-kirayen, inda suka ce kiran warewa gefen wani yunkuri ne na juyar da hankalin ‘yan jam’iyyar da kuma farautar wadanda suka dawo jam’iyyar.
Wata majiya daga zaman tattaunawar ta ce, “Muna sane da cewa, wadannan mutane dai sun yiwa jam’iyyar PDP takara a shekarar 2019 bayan sun dawo jam’iyyar.
“Idan a zaben shekarar 2019 babu wanda yai kiran a hana su takara, to a wane dalilin suke kiran da a dakatar da su a yanzu?
“Abune marar dadi cewa, wadansu mutane suna dauka kamar jam’iyyar PDP jam’iyyarsu da suka mallaka su su kadai.
“Ya kamata mu baiyana cewa, wadansu mutane ne suka gina PDP tun daga tushe har ta kawo yanda take a yanzu. Saboda haka mutane ya kamata su daina daukar kansu kamar sune suke mallakar jam’iyyar. Duk muna da gudunmawar da muka bayar daidai wa daidai a PDP.”
Da majiyar ke kara bayar da bayanan kariya, ta ce, wannan kiran ya saba da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin PDP da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, na a hana dan jam’iyya Takara a kowacce takarar da yake nema.
Wata majiyar ta sanar da cewa, lokacin da rudanin yai yawa, Shugaban Jam’iyyar Ayu ya yanke shawarar dage zaman.
Haka kuma, zaman kwamitin amintattu na jam’iyyar da zaman shugabannin jam’iyyar na kasa wadanda aka shirya gudanarwa a jiya, an cirasu zuwa yau domin a samu damar yin tuntuba.
(THE NATION)