Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Lagos (Lagos Chamber of Commerce and Industry (LCCI), ta yi kiyasin cewa, tsawon watanni bakwai na haramta amfani da manhajar Twitter a Najeriya, ya jawowa Najeriya asarar kudi Naira tiriliyan 10.72.
Babbar Daraktan LCCI, Dr. Chinyere Almona ce ta bayyana haka, a wani jawabi da yai ranar Juma’a a Lagos.
Cibiyar LCCI ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da yanayi mai kyau wanda ke goyon bayan tsare-tsaren kamfanonin fasahar zamani na duniya wajen samun nasararsu da kuma riba.
Da take sharhi kan cire haramcin Twitter a Najeriya da sauran abubuwa, Almona, ta ce, “sanarwar cire haramcin Twitter a Najeriya ya zo a daidai, kuma abin yabawa ne.
“A tsarin kasuwanci, asarar da haramcin tsawon watanni bakwai kan Twitter ya jawo ya kai naira tiriliyan 10.72, kamar yanda kididdigar Netblock’s Cost of Shutdown Tool ta bayyana.”
Almona ta kuma bayyyana cewa, kafafen sadarwar zamani sun kasance masu matukar tasiri wajen gudanar da kasuwanci da kuma gwamnati, musamman wajen mu’amula da mutane da kuma amfani da fasahar zamani a harkar kudade.
“Yanzu haka, bangaren Fasahar Yada Bayanai ta Zamani yana daya daga cikin harkokin kasuwanci mafiya girma a bangaren ciyar da tattalin arziki gaba.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wani lokaci a satin da yake karewa ne ya sanar da cire haramcin Twitter, watanni bakwai bayan sanya haramcin.
Ofishin Shugaban Kasa ya ce, hukuncin cire haramcin zai kara dankon alaka tsakanin bangarorin biyu, wadda za ta jawo cigaba mai ma’ana.