A kokarinta na samar da zaman lafiya a cikin al’umma, Rundunar Hisbah ta Jigawa ta shiga tsakani tare da sasanta rigingimun iyalai da na a’umma guda 4,231 a shekarar 2021.
Kwamandan Hisabah na jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan, yayin da yake gabatar da rahoton aiyukan hukumar na shekarar 2021 ga manema labarai a Dutse.
KU KARANTA: Jami’an Hukumar Kula Shige Da Fice Sun Kubutar Da Mutane 20 A Jigawa
Ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2021 rundunar ta sasanta rigingimun cikin gidaje guda 3,579 wanda suka shafi ma’aurata da kuma rigingimu 221 da suka shafi ‘ya’ya da iyayensu.
Kwamandan ya kuma bayyana cewa, rundunar ta samu nasarar sasanta rigingimu 71 wadanda suka shafi Makiyaya da Manoma wadda ta temaka wajen magance zubar da jini a yankin.
“Sauran rigingimu da muka sasanta sun hada da, sabani 41 kan matsalar bashi tsakanin masu saye da siyarwa da kuma sabani 319 tsakanin makwabta,” in ji shi.