Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama motoci hudu makare da giya mai yawan sama da kwalabe 4,200.
Babban Kwamandan Rundunar, Dr. Harun Ibb Sina ne ya baiyana hakan a Kano, yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a ranar Asabar.
Ya baiyana cewa, an kama motocin ne a kan titin Kwanar Dangora zuwa Kiru da kuma kan titin Zaria zuwa Kano.
Kwamandan ya kuma yi bayanin cewa, dokokin shari’a na jihar Kano sun sha da kuma siyar da giya da ma sauran kayan maye, inda ya jaddada cewa, an tanadi tsauraran hukunci ga duk wanda ya karya dokar.
Haka kuma, rundunar ta samu nasarar kama batagarin da suke harkar karuwanci, ta’ammali da miyagun kwayoyi, da sauran aiyukan da aka hana a Panshekara.
Ibn Sina ya kara da cewa, an kama matasan ne bayan an sami korafi daga wajen mazauna yankin.
Ya kuma koka bisa karuwar korafe-korafen shigar yara cikin abubuwan da kan haifar rikici da mugayen laifuka.
Ibn Sina ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kula sosai tare da fallasa duk wani wanda ake zargi a wajen hukumomin da suka dace.
Ya kuma tabbatar da shirin rundunar wajen hada guiwa da duk masu ruwa da tsaki domin a kawar da duk wasu batagari a jihar.