Wasu yara su uku sun mutu sandaiyyar nutsewa a kogin a kauyen Kazamaki, a yankin karamar hukumar Guri a jihar Jigawa.
Al’amarin ya faru ne lokacin da yaran suke yawon kiwon rakuma, inda suka nutse a lokacin da suke kokarin tsallake kogin.
Mai Magana da yawun ‘yansanda a jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu ya tabbatarwa jaraidar DAILY POST faruwar al’amarin.
KU KARANTA: Wanda Yai Garkuwa Da ‘Yar Shekara 5, Ya Kasheta Ya Daddatsa Gawarta
ASP Lawan ya ce, “Al’amarin ya farune a ranar 19 ga Janairu, 2022 lokacin da yaran masu suna: Musa Ahmad dan shekara 12, Yusuf Ahmad dan shekara 7 da kuma Alkasim Muhammad dan shekara 14 duk kaninsu ‘yan kauyen Fulani na Kazamaki a karamar hukumar Guri suke kokarin tsallake ruwan.”
“Ana karbar wannan rahoto, ‘yansanda suka ziyarci inda lamarin ya faru, inda aka ceto gawarwakin mamatan daga kogin aka kai su Babban Asibitin Hadejia, inda likita ya tabbatar da mutuwarsu.”
Ya kara da cewa, an mika gawarwakin ga ‘yan’uwan mamatan domin ai musu sutura yanda Addinin Musulunci ya tanada.
“Binciken farko ya nuna cewa babu hannun wani a cikin hatsarin, amma har yanzu ana cigaba da bincike akai,” in ji ASP Lawan Shiisu.
(DAILY POST)