Sabbin wadanda sukai rijistar katin zabe a fadin Najeriya sun kai miliyan tara da dubu dari biyu da talatin da takwas da dari tara da casa’in da daya (9, 238, 991) a daidai ranar Litinin din da ta gabata.
Bayanin wannan kididdiga ya fito daga Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa a jiya Talata.
Hukumar ta kuma baiyana cewa, masu rijista guda miliyan biyar, da dubu dari takwas da arba’in da biyar da dari bakwai da hamsin da ɗaya sun kammala rijistarsu.
A cikinsu, mutane miliyan biyu da dubu dari biyar da tamanin da hudu sun yi rijistar ne ta yanar gizo inda su kuma mutane miliyan uku da dubu dari biyu da sittin da ɗaya da ɗari biyu da uku suka yi rijistar kai tsaye.
Bayan na INEC ya kuma nuna cewa cikin waɗanda sukai rijistar, mutane miliyan biyu da dubu ɗari tara da uku da uku maza ne, yayin da kuma mutane miliyan biyu da dubu ɗari tara da arba’in da biyu suka kasance mata, sai kuma masu bukata ta musamman su su dubu arba’in da takwas da ɗari biyu da hamsin da biyu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa, bayanin shekarun waɗanda sukai rijistar ya nuna cewa mutane miliyan hudu da dubu arba’in da biyar da ɗari biyar da ashirin sun kasance matasa ne.
Sauran mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da ashirin da shida da ɗari biyar da hamsin suka kasance ƴan tsakanin shekaru 35 zuwa 49; sai kuma mutane dubu ɗari biyar da huɗu da ɗari biyu da ashirin da biyu suka kasance dattawa masu shekaru 50 zuwa 69, sai kuma mutane dubu sittin da tara da ɗari takwas da hamsin da tara suka kasance tsofi masu shekaru 70 zuwa sama.
Hukumar ta baiyana cewa ta karbi bukatun mutane miliyan sha shida da dubu ɗari takwas da hamsin da takwas da ɗari tara da hamsin da biyar ciki har da waɗanda ke buƙatar a sauya musu wajen yin zaɓe, sabunta musu katin, da kuma sauran gyare-gyare.
NAN