For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sabon Canji A Dokar Zabe Da Zai Hana ‘Yan-Kasa Kalubalantar ‘Yan-Takara

Wani sabon canji a gyaran dokar zabe na nuni da cewa, an cire damar dukkanin ‘yan-kasa ta iya kalubalantar tardun da dan-takara ya gabatarwa Hukumar Zabe a gaban kotu, kamar yanda PUNCH ta gano.

Sabuwar dokar, idan har Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu, zata bayar da damar kalubalantar takardun karatu, na haihuwa da sauransu ne kadai ga abokin takara a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyya.

A yanzu dai, Sashi na 31 (5) na Dokar Zabe ya ce, “Kowanne mutum da yake da hujja kakkarfa wanda yarda cewa bayanan da dan-takara ya gabatar ko takardun da wannan dan-takara ya gabatar ba na gaskiya ba ne, zai iya shigar da kara Babbar Kotun Tarayya, Babbar Kotun Jiha ko Babbar Kotun Birnin Tarayya yana kalubalantar wannan mutumin, yana bukatar a tabbatar da cewa wadannan bayanai da aka gabatar na karya ne.”

Sabon kudirin gyaran wannan sashi shi kuma yana cewa, “Kowanne dan-takara da ya shiga zaben fidda gwani a jam’iyyarsa, wanda yake da kwararan hujjoji da suke nuna cewa, bayanan da dan-takarar jam’iyyarsa ya gabatar ko takardun da wannan dan-takara ya gabatar la’akari da bukatar Kundin Tsarin Mulki kan abun da ake bukata ga dan-takara wajen tsayawa zabe, to zai iya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya yana kalubalantar wannan dan-takara, yana bukatar a tabbatar da cewa bayanan da ya gabatar na karya ne.”

A yanzu dai, dukkan dan-Najeriya yana da damar kalubalantar takardun ‘yan-takara na kowacce jam’iyya.

An sha tabbatar da wannan doka a hukunce-hukuncen da kotuna sukai a baya.

KU KARANTA: Zamu Bar Nigeria Sama Da Yanda Muka Sameta – Buhari

Misali a shari’a tsakanin Lawrence da PDP da kuma Ors (2017), Kotun Koli a hukuncin da alkalinta Walter Onnoghen ya karanta ya ce, “Tanadin doka daga Sashi na 31 (5) na Dokar Zabe ta 2010 kamar yanda aka sabunta, babu makawa cewa, ya bayar da dama gamammiya ga kowa, ko dan-jam’iyya ko ba dan-jam’iyya ba ya nemi Babbar Kotun Tarayya kamar yanda tanadin dokar ya ce, kuma kotun tana da cikakkiyar dama ta sauraro da kuma yanke hukunci kan karar da ya shigar.”

Da take tabbatar da hukuncin ita ma, Babbar Alkaliya Kudirat Kekere-Ekun ta ce, “Sashi na 31 (5) na Dokar Zabe ta 2010 wadda aka sabunta, ya baiwa kowa dama, wanda yake da kwararan hujjoji da suke nuni da cewa, bayanan da dan-takara ya gabatar ba gaskiya ba ne, ya shigar da kara gaban Babbar Kotu yana bukatar a tabbatar da cewa wadannan bayanai ba gaskiya ba ne.”

A shekarar 2019, jam’iyyar PDP da dan-takararta na gwamna a jihar Bayelsa, Douye Diri; sun shigar da karar dan-takarar gwamna na jam’iyyar APC, David Lyon da mataimakinsa, Biobarakuma Deqi-Eremienyo, suna bukatar a hana takararsu saboda matsalar takardun Degi-Eremienyo.

A wannan lokacin Kotun Koli ta amince da bukatar PDP inda ta haramta takarar wadanda aka zarga duk da kasancewar INEC ta riga ta bayyanasu a matsayin wadanda suka ci zabe.

Da a ce a wannan lokacin wannan sabon canjin dokar yana nan, abun da ya faru a Bayelsa ba zai faru ba.

Comments
Loading...