Daga: Ahmed Ilallah
Tabbas Jama’iyar APC tayi rawar ganin ta yadda ta samu gagarumar nasara a zaben Shugaban Kasa da kuma yan Majalissar Dokokin Tarayya, musamman ma a Jihar Jigawa.
Jihar Jigawa tana daga cikin muhimman jahohin da Jama’iyar APC ta ke tunkaho da su a Najeriya.
Mutanen Jigawa sunyi imani da Jama’iyar APC, sun ci wa APC zaben tun kafin zaben gamagari na 2015.
A 2014 zaben kananan hukumimin Jihar Jigawa, mutane Jigawa musamman na kananan hukumomin Hadejia da Malam Madori sun lashe zaben majalissun kananan hukumomin su, amma gwamnatin PDP karkashin Sule Lamido ta soke zaben, sannan ya nada musu kantomomi.
Jihar Jigawa tun daga wannan lokacin ta ke bada gudumawar habakar Jama’iyar APC, madalla da jagoranci Gwamna Badaru Abubakar.
Lokaci yayi da jagoranci Jama’iyar APC da zababbun ‘yan Majalissar Tarayyarta 10 da su sakawa Jihar Jigawa, su zabi daya daga cikin ‘ya’yansu ya zama shugaban Majalissar Wakilai (Speaker), a wannan Majalissar ta 10.
A kwai kwararrun wakilai da suka koma wannan Majalissar a karo na uku kuma kai tsaye, suna da kwarewa da iya siyasa da kuma ilimin da ya kamata a basu damar shugabancin wannan Majalissa.
Hon. Zama Fulata mai wakiltar Birniwa, Guri da Kiri Kassamma, tsoho kuma kwararren dan siyasa, tsohon malamin jami’a mai digirin digirgir, wanda a yanzu a ka zabe shi a karo na uku kuma kai tsaye a wannan Majalissar, ya cancanci ya zama shugaban wannan Majalissar a wannan karon.
Bayan Hon. Zama Fulata, da yawa sun koma wannan Majalissar a karo na uku daga Jihar Jigawa, irin su Hon. Kamfani Auyo, Hon. Miga da irin su Hon. Makki Abubakar, Hon. Sani Fulawa wanda duka sun dawo wannan zaure a karo na biyu.
Lokaci yayi da za a mara wa mutumin Jigawa ya jagoranci wannan Majalissar.
Ya kamata a sakawa mutanen Jigawa, a goyi bayan Hon. Fulata don zama shugaban Majalissar Wakilai ta goma.
alhajilallah@gmail.com