For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sabuwar Dokar Aiki Zata Jawo Rasa Aiki Ga Daraktoci 512 A Najeriya

Kusan daraktoci 512 da ke aikin gwamnati ne waɗanda suka ɗebe shekaru 8 a matsayin darakta zasu fuskanci barin aiki saboda fara amfani da sabbin Dokokin Aikin Gwamnati na shekarar 2021 daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya.

Sabbin Dokokin Aikin Gwamnatin da suka fara aiki a ranar 27 ga watan Yuli, 2023, sun samu ƙaddamarwa ne daga ofishin Shugabar Ma’aikata ta Ƙasa a ranar 28 ga watan Yuli, 2023 a Abuja.

Sabbin dokokin sun kuma zo da tsarin wa’adi ga manyan sakatarorin gwamnati, waɗanda a yanzu suke da wa’adin shekaru huɗu a ofis wanda za a iya sabuntawa bayan an yi nazarin ƙoƙarin ma’aikaci.

Majiyoyi daga ofishin Shugabar Ma’aikata ta Ƙasa sun tabbatar wa da wakilin PUNCH a ranar Alhamis cewa, sabbin dokokin zasu taɓa kwatankwacin daraktoci 512 waɗanda suka tsaya a matsayin darakta tsawon shekaru takwas ko sama da haka.

Shugabar Ma’aikata ta Ƙasa, Folashade Yemi-Esan, a yayinda take ƙaddamar da sabbin dokokin a makon jiya, ta tabbatar da cewa, sabbin dokokin zasu fara aiki nan take.

Yemi-Esan ta bayyana cewa, an sabunta dokokin ne tun a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, amma an dakatar da ƙaddamar da su, sai a zamanin mulkin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin su dace da manufofin gwamnatinsa.

Sabbin dokokin dai sun jawo gunaguni a tsakanin wasu ma’aikatan gwamnati, inda wasu suka tabbatar da cewar an tura sabbin dokokin ga ma’aikatu domin fara ɗabbaƙa su.

Comments
Loading...