For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sahihin Jerin Sunayen Ministocin Tinubu Da Sanatoci Suka Aminta Da Su

Majalissar Sanatoci ta kammala tantance mutane 45 cikin 48 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mata a ƙoƙarinsa na naɗa su ministoci.

Sanatocin sun tabbatar da amincewarsu da mutane 45 ɗin ne a jiya Litinin 7 ga watan Agusta, 2023.

Uku cikin waɗanda shugaban ƙasa ya miƙa sunayensu ba su sami tsallakewar tantancewar sanatocin ba har kawo wannan lokacin saboda zarge-zargen tsaro a kansu, sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Stella Okotette daga Jihar Delta da Abubakar Danladi daga Jihar Taraba.

Sanar da amincewar sanatocin dai na zuwa ne cikin sama da mako guda bayan Shugaba Tinubu a ranar 27 ga Yuli, 2023, ya miƙa jerin sunayen farko ga majalissar adomin tantancewa.

Ministocin da sanatocin suka aminta da su sune:

  1. Abubakar Kyari (Borno)
  2. Abubakar Momoh (Edo)
  3. Nyesom Wike (Rivers)
  4. Engr Joseph Utserv (Benue)
  5. Senator John Owan Enoh (Cross River)
  6. Hon Bello Mohammad (Sokoto)
  7. Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa)
  8. Amb. Yusuf Maitama Tuggar (Bauchi)
  9. Uju Kennedy Ohaneye (Anambra)
  10. Hon. Olubunmi Tunji-Ojo (Ondo)
  11. Nkieruka Onyejeocha (Abia)
  12. Dr Betta Edu (Cross River State)
  13. Imaan Sulieman Ibrahim (Nasarawa)
  14. David Umahi (Ebonyi)
  15. Adebayo Olawale Edun (Ogun)
  16. Arch. Ahmed Musa Dangiwa (Katsina)
  17. Chief Uche Geoffrey Nnaji (Enugu)
  18. Mr Dele Alake (Ekiti)
  19. Waheed Adebayo Adelabu (Oyo)
  20. Mohammed Idris (Niger)
  21. Prof Ali Pate (Bauchi)
  22. Dr Doris Anite Uzoka (Imo)
  23. Lateef Fabemi SAN (Kwara)
  24. Rt Hon Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom)
  25. Hannatu Musawa (Katsina)
  26. Ibrahim Geidam (Yobe)
  27. Aliyu Sabi Abdullahi (Niger)
  28. Hieneken Lokpobiri (Bayelsa)
  29. Alkali Ahmed Saidu (Gombe)
  30. Dr Tanko Sununu (Kebbi)
  31. Atiku Bagudu (Kebbi)
  32. Bello Matawalle (Zamfara)
  33. Adegboyega Oyetola (Osun)
  34. Simon Bako Lalong (Plateau)
  35. Abdullahi Tijani Muhammad Gwarzo (Kano)
  36. Bosun Tijani (Ogun)
  37. Dr Mariya Mahmoud Bunkure (Kano)
  38. Dr Iziaq Salako (Ogun)
  39. Dr Tunji Alausa (Lagos)
  40. Lola Ade-John (Lagos)
  41. Prof Tahir Mamman SAN (Adamawa)
  42. Zephaniah Jisalo (FCT)
  43. Uba Maigari Ahmadu (Taraba)
  44. Prince Shuaibu Abubakar Audu (Kogi)
  45. Festus Keyamo SAN (Delta)
Comments
Loading...