Jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP ta ce, jam’iyyar na kara samun haske na samun cin zabe a babban zaben shekarar 2023.
Shugaban Jam’iyyar na Jihar Jigawa, Gambo Ibrahim Alawo ne ya baiyana hakan ga manema labarai jiya, bayan taron jam’iyyar na jihar da aka gudanar a Dutse.
Ya ce, wannan na zuwa ne a yayin da jam’iyyar ke sa ran karbar sabbin mambobi a dukkanin fadin kasa saboda gazawar jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP wajen share hawayen ‘yan Najeriya.
Alawo ya baiyana cewa, NNPP ta shirya tsaf domin bayar da dama ga duk dan Najeriya wajen nuna ‘yancinsa na demokaradiyya dai-dai da bukatar jam’iyya da kuma tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
Ya kuma shawarci wadanda suka nuna sha’awar shiga jam’iyyar da su bi hanyar da ta dace wajen yin rijista domin gujewa yin kuskuren da zai iya jawowa jam’iyyar rashin nasara a zabubbuka masu zuwa na shekarar 2023.
“Sama da mutane 300,000 ne daga jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP da jam’iyya mai mulki, All Progressive Congress, APC, da sauran jam’iyyu za su shiga jam’iyyarmu kwanan nan a Jihar Jigawa.
“Mun yi farinciki matuka da cigaban da aka samu, mun shirya tsaf domin yin maraba da su zuwa jam’iyyarmu, saboda haka mun yi alkawarin samar da yanayi mai kyau da kuma yin mu’amala da su cikin gaskiya da adalci.”
Shugaban Jam’iyyar ya nuna cewa, duba da yanayin da ake ciki yanda kasar take tafiya a hannun PDP da APC, ‘yan Najeriya na bukatar jam’iyyar da za ta magance matsalolin kasar tare da maido mata da martaba.
Saboda haka ya yi kira ga ‘yan Jihar Jigawa wadanda kewa jihar fatan alkhairi da ‘yan Najeriya wadanda kewa kasar fatan alkhairi da su shiga jam’iyyarsu ta NNPP domin samun ingantacciyar Najeriya.
Daga: Bala Ibrahim