Kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU ta ce, Gwamnatin Tarayya ba ta yi gyara ga albashin malaman jami’o’i ba
tsawon sama da shekaru 13 tun bayan yarjejeniyar 2009.
Shugaban Kungiyar ASUU reshen Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ATBU, da ke Bauchi, Dr. Ibrahim Ibrahim Inuwa ne ya baiyana hakan a jiya, inda ya ce a yarjejeniyar shekarar 2009 an amince da cewa, duk bayan shekaru 3 za a yi gyara ga albashin malaman jami’o’i gwargwadon tattalin arziki da kuma darajar naira.
Dr. Ibrahim ya ce, cikin tsawon shekaru 13, gwamnati ta bayar da naira biliyan 200 a zamanin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan daga yarjejeniyar shekarar 2009.
Ya baiyana cewa, abubuwan da ke tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya sun hada da yarjejeniyar 2009, kudaden gyaran jami’o’i, tilasta shiga IPPIS, da yawaitar jami’o’i da sauransu.
“Mun samar da kwamiti. Bangarori biyu sun duba rahoton kwamitin da suka hada da ASUU da Gwamnatin Tarayya. Sai da ya kawo matsayin kowanne kwamiti ya koma ga jagororinsa, amma gwamnati ta mika rahoton ga wani kwamitin na daban don ya kara dubawa. Bayan nan bangaren gwamnati ya yi ikirarin mika rahoton ga Shugaban Kasa domin ya sanya hannu. Gwamnati tana ta jan kafarta, amma dai za mu cigaba da matsawa. . .”
Dr. Ibrahim ya kuma ce, sama da malaman jami’a 13 ne a reshen ASUU na ATBU da ba su sami kudaden alawuns dinsu na ciyarwa gaba ba, wanda ya kai tsawon tsakanin watanni 15 zuwa 20.
Da yake mayar da martani kan rokon da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ga ASUU na ta dakatar da shirinta na shiga yajin aiki, Dr. Ibrahim ya ce, babu bukatar shugaban ya yi haka, kawai ya mayar da hankali kan matsanancin halin da ilimi da malaman jami’o’i ke ciki.
Ya yi kira ga malaman addini da sarakunan gargajiya da su yi kira ga gwamnati da ta yi abun da ya kamata.