For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sama Da Ƴan Afirka Miliyan 300 Ne Ke Kwana Da Yunwa A Kullum

Bankin Fitarwa da Shigarwa da Kayayyaki na Afirka, Afrixembank ya ce, sama da ƴan Afirka miliyan 300 ne ke kwana da yunwa a kullum.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya bayyana cewa, Shugaban Daraktocin Bankin Afreximbank, Dr. Benedict Oramah ne ya bayyana hakan a lokacin buɗe taron Ƙungiyar Rasha da Afrika kan Tattalin Arziƙin Da Temakon Ɗan’adam.

Oramah ya ce, mafi yawan mutanen Afirka sun dogara da ƙasar Rasha a ɓangaren takin zamani, haka kuma kaso 30 cikin 100 na tsabar da ake shigowa da ita Nahiyar Afirka, ana shigo da ita ne daga Rasha.

Labari Mai Alaƙa: BAIWA MATA TALLAFI A JIGAWA: Da Muguwar Rawa Gwamma Ƙin Tashi, Shawara Ga Gwamna Namadi

Ya kuma yi fatan samun ingantaccen tsarin kasuwanci tsakanin Rasha da ƙasashen Afirka.

Oramah ya ƙara da cewa, bankin Afrixembank ya tanadi kuɗi dala biliyan 3 domin sanya hannun jari a samar da abinci tsakanin Rasha da Afirka.

“Dala biliyan ukun, sune abun da aka ware, kuma za a yi amfani da su akai-akai domin temakawa buƙatar samun abinci da takin zamani ga Afirka.

“Yana da matuƙar amfani cewa duk ɗinmu mu yi abin da ya dace wajen tabbatar cewa, sai an samar da wadatar abinci kafin komai,” in ji shi.

Comments
Loading...