For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sanata Kabiru Gaya Ya Ce, Mayar Da Mulki Kudancin Najeriya Shi Ne Adalci A APC

A Najeriya, yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da dan Arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa, wani dan Majalisar Dattawa daga jam’iyyar APC mai mulki ya ce, kamata ya yi jam’iyyarsu ta tsayar da wani daga kudancin kasar.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, wanda dan Jihar Kano ne da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya ce, bai wa yankin kudanci takarar shi ne babban alheri da adalci ga APC, kuma a cewarsa zai sa ta ci zabe a 2023.

Wannan na zuwa ne, yayin da rahotanni ke cewa akwai zaman dar-dar a jam’iyyar ta APC gabanin zaben fid da dan takarar shugaban kasa.

Bayan shugaba Muhammadu Buhari ya tara gwamnonin jam’iyyarsu, tare da shaida musu cewa ya zabi wanda zai gaje shi kuma yana son su goya masa baya domin ya samu tikitin tsayawa takara, abin da aka ce bai yi wa wasu gwamnonin dadi ba.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya shaidawa BBC Hausa cewa, “Ita siyasa, ko duk rayuwar duniya alkawari ce. In ka yi wa dan Adam alkawari to ka cika alkawarin da kayi da shi. An yi alkawari da Kudu, sun amince Buhari ya yi mulkin shekara takwas, ya kamata kuma a mika musu, domin su ma su yi shekara takwas.”

Da aka tambaye shi cewa babu wanda ya ga wannan yarjejeniyar karba-karba kuma ba ya cikin tsarin mulki, sai ya ce, “Ai na san ba rubutawa aka yi ba, amma idan ka yi alkawari da mutum, ko da baki ne ba sai ya rantse maka ba”.

Ya kuma tabbatar da cewa, a ganinsa takara Kudu zata tafi a jam’iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya.

“In sha Allah Kudu za ta, domin shi ne alheri ga APC, kuma shi ne alheri ga Najeriya. Su ma ‘yan Kudun ‘yan Najeriya ne, bai dace a ce kullum sai Arewa ce za ta yi mulkin Najeriya ba.”

Ya ce ba yana nuna kiyayya ga arewacin kasar ba ne, amma ya ce adalci shi ne ginshiki, inda ya kara da cewa idan aka sami adalin shugaba, ko daga ina ya fito sai a mara masa baya.”

A halin da ake ciki, jam’iyyar ta APC ta kammala tantance masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a inuwarta a ranar Talatar da ta gabata.

Abin da ya rage ma ta, shi ne zaben fidda gwani, kafin ta tunkari babban zaben da ke tafe a shekara mai zuwa.

Abin jira a gani shi ne, ko gwamnonin APC za su yi wa Shugaba Muhammadu Buhari biyayya ta hanyar yi wa dan takarar da ya zaba mubaya’a kamar yadda a kullum suke fadin su na yi masa biyayya ko akasin haka.

(BBC Hausa)

Comments
Loading...