For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sanatoci Sun Amince Su Sanya Hannu A Dokar Zabe

Sanatoci da dama sun yi alwashin kaucewa Buhari wajen sanya hannu a dokar zabe bayan Shugaba Buhari ya ki sanyawa dokar hannu.

Jaridar PUNCH ta fahimci hakanne daga kokarin da ta gano Shugaban Majalissar Dattawan Ahmad Lawan na yin kokarin kare Buhari daga jin kunya.

Lokacin da Ahmad Lawan ya karanta wasikar Buhari a majalissar a jiya, Sanata George Sekibo ya bayar da shawarar cewa majalissar ta shiga zaman sirri domin tattauna maganar.

Shugaban majalissar ya amince da kudirin inda aka fara zaman majalissar na sirri nan take wanda ya kwashe mintuna 37 ana gabatarwa.

Sanata Sekibo, wanda dan jam’iyyar PDP ne, bayan zaman ya shaidawa manema labarai cewa, majalissar ta dage zamanta ne domin bayar da dama ga dattawan su rinjayi shugaban kasa wajen sanya hannu a dokar.

Ya bayya cewa, “a dokance, muna da karfin iya sanyawa dokar hannu. Shine abin da sashi na 58 (4 da 5) suka bayyana. Za mu yi amfani da karfinmu mu yi hakan. Suna cewa sai mun hadu wajen amincewa da kudirin. Dokokinmu sun ba mu damar amincewa da doka ta hanyoyi guda 3; ta hanyar magana, ta hanyar sanya hannu da kuma ta na’ura. Saboda haka za mu iya amfani da kowanne. Mun karbi sa hannu a zaman kuma an samu daga mabanbantan jam’iyyu.”

Sanata Sekibo, bayan hakan, ya tabbatarwa gidan talabishin na CHANNELS cewa, sun tattara sa hannun sanatoci 73 domin sanya hannu a dokar.

JAKADIYA PRESS ta yi nazarin cewa, idan har ya tabbata adadin da Sanata Sekibo ya fada sun amince da dokar zaben a matsayin sanya mata hannu, to za a iya cewa Majalissar Dattawan ta amince da dokar.

Wani Sanata wanda dan jam’iyyar APC ne, ya ce shugaban majalissar bai aminta da sanya hannu a dokar ba, ya kuma bukaci ‘yan majalissar su dawo a yau Laraba kan batun.

Comments
Loading...