For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sanatoci Sun Yi Watsi Da Buƙatar Tinubu Ta Yaƙar Jamhuriyar Nijar

Sanatocin Najeriya sun yi watsi da buƙatar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya don su kai ɗauki wajen kawar da waɗanda su ka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Wanna dai ya kawo ƙarshen shirye-shiryen da sojojin Najeriyar ke yi na shiga yaƙi da maƙwabtansu sojojin Nijar a daidai lokacin da wa’adin kwanaki bakwai na dawo da mulkin demokaraɗiyya a Nijar da ƙungiyar ECOWAS ta bayar ke dab da cika.

Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya kushe juyin mulkin da aka yi a Nijar, amma kuma, ya yi kira ga Tinubu da yai amfani da wasu hanyoyin waɗanda zasu mutunta zumuncin da ƴan Najeriya da Nijar suka daɗe suna mora tsawon shekaru.

Akpabio ya ce, sanatocin sun fahimci cewar, Tinubu ba yana neman izininsu ba ne don ya shiga yaƙi da Nijar, sai dai ya tura musu takarda ne domin ya samu goyon bayansu wajen aiwatar da rahoton bayan taron ƙungiyar ECOWAS da ya gabata.

Ya ƙara da cewa, sanatocin zasu ci gaba da tattaunawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan hanyoyi mafiya inganci da za a bi wajen magance matsalar ƙasar Nijar ba tare da an ɓata zumuncin tsakanin ƙasashen biyu ba.

Godswill Akpabio dai ya yi waɗannan maganganu ne bayan fitowa daga zaman sirri na awanni biyu da Majalissar Dattawan ta yi a yau Asabar.

Makonni biyu da suka gabata ne, sojoji ƙarƙashin Janar Abdouramane Tchiani suka kifar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijar, Mohammed Bazoum a wani juyin mulki da suka yi.

Janar Tchiani dai ya samu goyon bayan ƙasashen Mali da Burkina Faso, sannan kuma ya yanke alaƙa da Najeriya, Amurka, Togo da kuma Fransa.

Comments
Loading...