For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sarkin Daura Zai Nada Ameachi Dan Amanar Daura

Daga: Haruna Bultuwa

Za a nada Ministan Sufuri Rotimi Ameachi Dan Amanar Daura ranar 5, ga watan Fabarairu na wannan shekarar, saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Eric Ojiekwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce za a karrama Ameachi ne, musamman a kokarin da ya yi na ganin an farfado da harkar sufurin jiragen kasa da ta shafe sama da shekaru 30 ana fama da ita.

Ya kara da cewa, Sarkin Daura, Umar Farouk Umar, zai yi bikin nada rawani a Fadar Sarkin Daura, da ke Daura a jihar Katsina, ranar Asabar, 5 ga Fabarairu da misalin karfe 11:00 na safe.

“Babban abin da za a yi a bikin shi ne nadin sarautar don karrama Minista da manyan baki da aka gayyata,” in ji shi.

Comments
Loading...