Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi mai murabus, ya koma aji a matsayin dalibi mai karatun digirin digirgir a fannin Shari’ar Musulunci a Jami’ar London da ke Birtaniya.
Sarki Sunusi wanda ya baiyana hakan ga jaridar editan PREMIUM TIMES a ranar Litinin, ya ce yanzu haka ya koma London da zama domin gudanar da karatun.
A baya dai, a shekarar 2019, Sarki Sunusi ya sami kyautar digirin digirgir na girmamawa a fannin hada-hadar kudade daga Sashin Nazarin Tarihi da Nahiyar Afirka na Jami’ar London.
Sarki Sunusi, a shekarar 1997, ya sami digiri a fannin Ilimin Addinin Musulunci da Fiqhu daga jami’ar Africa International University, da ke birnin Khartoum, na kasar Sudan.
Sarkin mai murabus, wanda a shekarar 1981 ya samu digiri a fannin Tattalin Arziki, a kwanan an ba shi damar zama malami mai ziyara a sananniyar jami’ar nan ta Oxfor, wato Oxford University da ke Birtaniya.
Sunusi, wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne, wanda kwadayin neman iliminsa ya bayyana, na daya daga cikin mutanen da sukai sarautar gargajiya suna da ilimi mai zurfi.
Sarkin ya bayyana cewa, yanzu haka yana hada karatunsa na digirin digirgir, PhD da kuma aikin koyarwar da yake a jami’ar Oxford.
Malami mai Ziyara
Watanni biyar bayan an yi masa murabus daga sarautar Kano a shekarar 2020, Sarki Sunusi ya nemi aikin koyarwa a jami’ar Oxford, sashin Nazarin Nahiyar Afrika, wanda jami’ar ta amince.
Aikin na Sarki Sunusi wanda aka tsara zai fara a watan Oktoba na shekarar 2020, zai debe tsawon shekara guda yana gudanarwa.
Ba a bayyana cewa ko aikin zai haura wannan lokacin ko kuma zai tsaya iya haka.
Sashin Nazarin Nahiyar Afirka na Jami’ar Oxford na a matsayin daya daga cikin Cibiyoyin da ke horas da dalibai kan Nahiyar Afirka, haka kuma ya horas da dalibai da dama wadanda a yanzu haka suna rike da muhimman mukamai a bangarori da dama na rayuwa, tattalin arziki, da kuma siyasar Nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya.
Cibiyar na da karfi a fannin nazarin rayuwar dan’adam da zamantakewa, wannan ya ba ta nasarar samun daukaka saboda inganci, binciken da ya dace wanda ya ke ba da gudumawa wajen cigaban ilimi da samar da tsare-tsare.
Jaridar ThisDay ta rawaito cewa, Cibiyar ta sanar da cewa, a lokacin da Sunusi yake aikinsa zai amfani da lokacin wajen rubuta littafinsa kan irin abubuwa da ya fuskanta a matsayinsa na gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Daga: PREMIUM TIMES