For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sau 50 Aka Kai Hare-Hare A Ofisoshin INEC Daga Shekarar 2019 Zuwa Yanzu

Shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce tun daga shekara ta 2019 zuwa yanzu an kai hari kan ofisoshin hukumar sau 50 a jihohi 15 cikin jihohi 36.

Ya bayyana hakan ne a yau Juma’a lokacin da yake bayani ga kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike a kan barnar da aka yi wa hukumar ta INEC.

A cewar Farfesa Yakubu an kai hari sau takwas a shekara ta 2019 a ofisoshin INEC, sau 22 a shekarar 2020, sau 12 a shekarar 2021 sannan kuma a shekarar 2022 an kai harin sau takwas.

Mafi yawancin hare-haren an kai su ne a jihohin da ke kudancin Najeriya, yayin da Shugaban INEC din ya ce an fi kai hare-haren a kan ofisoshin hukumar a jihar Imo inda aka kai sau 11 sannan kuma sai jihar Osun inda aka kai hari sau bakwai.

Farfesa Yakubu ya ce duk da irin wadannan matsalolin, suna ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da suka kamata domin tsara zabe mai inganci a shekara mai zuwa.

BBC Hausa

Comments
Loading...