For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Saudiyya Ta Ce Da Gaske Take Wajen Sasantawa Da Iran

Kasar Saudiyya ta ce da gaske take game da tattaunawar da take yi da kasar Iran, wadda ita ce babbar abokiyar gabarta a yankin.

BBC Hausa ta rawaito cewa, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yerima Faisal bin Farham Al-Saud, ya fada wa jaridar Financial Times cewa akwai fahimtar juna a tattaunawar da suka yi karo na hudu kuma ta yi tasiri.

Bambance-bambancen da ke tsakanin Saudiyya wadda galibin ‘yan kasar ‘yan Sunni ne da kuma Iran wadda ‘yan Shi’a suka fi rinjaye, su ne suka ruruta rikici da ake fama da shi a yankin na taswon shekaru.

Masu sharhi sun ce tattaunawar neman sulhu ta baya-bayan nan tsakaninsu ta nuna cewa kasashen a shirye suke su kawo karshen tashin hankali a yankin.

Comments
Loading...