Jamíyya mai mulki, All Prgressives Congress, APC, da mai yi mata takarar shugabancin kasa, Bola Ahmed Tinubu, har kawo yanzu ba su bayyana manufofinsu (manifesto) ba, kwanaki 20 kafin ranar fara yakin neman zabe a hukumance ga dukkan jam’iyyu domin shiga babban zaben shekarar 2023.
Shi dai manifesto wani tsari ne rubutacce wanda jam’iyyar siyasa ke tallata manufofinta da shi, da abubuwan da take so ta cimma, kuma abun da zata tallata kanta da shi a lokacin yakin neman zabe.
Ana bayyana shi ga al’umma domin masu zabe su gane shirye-shiryen jam’iyya game da kasa da kuma abun da zasu tsammata idan har su baiwa wannan jam’iyyar dama.
A baya dai Tinubu ya yi watsi da wani rubutu da ake yadawa wanda wasu makusantanta suka samar a matsayin manufofinsa.
Daraktan Harkokin Yada Labarai na Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga, a wani jawabi ya ce, “Asiwaju Tinubu yana ganawa da jam’iyya, masana a bangarori da dama da kuma dinbin ‘yan kasa, ta hanyar tsari mai kyau, yana aiki a kan manufofin da zai gabatarwa ‘yan Najeriya idan ya kammala kafin ranar da za a fara yakin neman zabe.”
A manyan zabubbukan shekarun 2015 da 2019, manufofin jam’iyyar APC sun kasance ne kan samar da tsaro, magance cin hanci da rashawa da kuma bunkasa tattalin arziki.
Game da babban zaben 2023, ‘yan Najeriya sun kagu da su ji abun da jam’iyyar zata gabatar a matsayin manufofinta wadanda suka saba da na baya, duba da yanayin da ake ciki a bangarorin da jam’iyyar tai alkawarin kawo gyara.
To sai dai kum, wasu gagga a jam’iyyar da sukai magana da jaridar DAILY TRUST sun ce, jam’iyyar zata kara gabatar da kudirin magance matsalar cin hanci da rashawa, magance matsalar tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.
Wani jigo a jam’iyyar kuma Babban Daraktan Voice of Nigeria, VON, Osita Okechukwu a hirarsa da DAILY TRUST a jiya ya ce, “Duk wasu manufofin da dan takarar shugaban kasar jam’iyyarmu zai samar, zai zama an ciroshi ne daga manufofin APC. Bana tunanin zamu samu wasu manufofi da suka saba da manufofin jam’iyya.”
Haka kuma, mamba a Kwamitin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, NEC, kuma tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labarai, Yekini Nabena ya ce, “Ka sani nima na sani manyan matsalolin wannan kasar sune rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da tattalin arziki. Saboda haka, bana tunanin za a samun wani canji daga abubuwan 2015 da na 2019 na yakin neman zabe.”