For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

SERAP Na Bukatar Kotu Ta Soke Yafiyar Da Buhari Yai Wa Joshua Dariye Da Jolly Nyame

Kungiyar Tabbatar da Hakkokin Rayuwa da Aiwatar da Gaskiya ta SERAP ta shigar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kara kan yafiyar da yai wa tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Sanata Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame.

An dai binciki tare da kama Dariye da Nyame saboda satar kudaden jihohinsu Naira Biliyan 1.16 da Naira Biliyan 1.6 lokacin suna gwamnonin jihohin a tsakanin shekarar 1999 da 2007 bayan sun bar ofis a shekarar 2007.

A ‘yan makwannin da suka gabata ne dai Shugaba Muhammadu Buhari yai musu afuwa tare da wasu mutane 157.

A karar da SERAP ta shigar ranar Juma’a a Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Lagos, ta bukaci kotun da aiyana yafiyar da akai wa tsohon Gwamnan Plateau, Sanata Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Taraba Rabaran Jolly Nyame, a matsayin wadda ta saba doka da kuma rantsuwar kama aiki, da ma ra’ayin jama’a.

A cikin sanarwar da aka saki ranar Lahadin da ta gabata, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare ya ce, SERAP na bukatar kotu ta aiyana cewa, gudanar da aiki da kuma karfin iko na yin yafiya ga Dariye da Nyame ya sabawa bukatar ‘yan kasa, rantsuwar shiga ofis, da kuma nauyin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa na yaki da cin hanci da rashawa.

A karar, SERAP ta ce, idan har ba a ajjiye batun yafiyar nan a gefe guda ba, cin hanci da rashawa zai karu, kuma manyan ‘yan siyasa da dama zasu na gujewa hukunci kan laifukan da ake zarginsu.

SERAP na kuma bukatar kotu ta bayar da umarni ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugabannin kasa masu zuwa da suna kulawa da abin da zai amfani ‘yan kasa, rantsuwar kama aiki, da kuma aikin da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su na magance matsalar cin hanci da rashawa a duk lokacin da zasu yi afuwa ga wasu.

Cikin wadanda SERAP ke tuhuma har da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN).

Babu dai takaimaimiyar ranar da aka saka domin sauraron karar a halin yanzu.

Comments
Loading...