A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, masu gabatar da kara sun ce sun kammala gabatar da shaidunsu a ranar Laraba a shari’ar dan kasar Chinan nan wanda ake zargi da kashe wata matashiya mai suna Ummita.
Sai dai sun ce ba su shirya tunkarar shaidun wanda ake zargin ba, inda alkalin babbar kotun ya dage zaman zuwa ranar juma’a mai zuwa.
BBC Hausa ta rawaito cewa, babbar kotun, ta saurari shaida na karshe daga bangaren masu gabatar da kara a shari’ar zargin da ake yiwa Geng Quangrong dan kasar China, da kashe tsohuwar budurwarsa Ummulkhuksum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Shaidar wani dan sanda ne, Aminu Halilu inda ya tabbatar wa da kotu cewa ranar 16 ga watan Satumbar 2021 shi ne ya dauki bayanan wanda ake tuhuma sannan ya sanya hannu kan takardar.
Sai dai lauyan Mista Geng, ya ce tilasta masa aka yi fadin abin da aka rubuta tare da tilasta masa sanya hannu, aka kuma hankaɗa shi cikin sel aka kulle.
Don haka lauyan ya ce basu amince da bayanan da aka gabatar ba a ciki har da takardun asibiti.
To sai dai mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya amince da bayanan shaidar a matsayin exhibit C, ko da yake ya ce idan ya bincika ya gano tursasa wanda ake zargin aka yi, domin ya bayar da bayanan a caji ofis to zai yi watsi da bayanan.
Sannan ya kuma amince da bayanan asibiti da bangaren masu kara suka gabatar, kuma shi ne abin da ya haifar da jayayya da dogon turancin da har sai da aka tafi hutu.
Sai ranar Juma’a ne 23 ga wannan watan nan, ɗan ƙasar Chanan nan zai fara gabatar da shaidunsa a shari’ar da ake yi masa kan zargin kashe Ummita.