For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sheikh Ibrahim Khalil Ya Shiga Jam’iyyar ADC

Sanannen Malamin Addinin Musuluncin nan kuma Shugaban Majalissar Malamai na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress, ADC.

Shugaban Jam’iyyar ADC na jihar Kano, Musa Shuaibu Ungogo ya tabbatar da shigar malamin cikin jam’iyyar ga jaridar NIGERIAN TRACKER.

Shugaban jam’iyyar ya ce, Sheikh Ibrahim Khalil ya shiga jam’iyyar ne tare da Farfesoshi 8 domin su kubutar da jihar Kano daga mummunan shugabanci, shaye-shaye da bara.

Musa Shuaibu Ungogo ya kara da cewa, ofishin jam’iyyar ADC na kasa kwanannan zai shirya gagarumin taro na musamman domin karbar Sheikh Ibrahim Khalil da sauran wadanda suka shiga jam’iyyar.

Comments
Loading...