For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shekarau Ya Fice Daga APC Ya Koma NNPP

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin Najeriya.

Malam Shekarau ya shiga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP kamar yanda jaridar PUNCH ta rawaito.

Tsohon Darakta Janar na Gungun Magoya Bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Abdulmumin ya rubuta a Twitter cewa, “YANZU-YANZU – Sanata Ibrahim Shekarau ya shiga NNPP. Sauran bayani na tafe.”

Daga baya, jam’iyyar NNPP ta saki hotunan ziyarar jagoran NNPP na ƙasa, Kwankwaso inda ya je gidan Shekarau.

Jam’iyyar ta wallafa a Twitter cewa, “Maigirma Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar taya murna ga tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau bayan ya shiga jam’iyyar NNPP.”

A yanzu haka dai, Shekarau shine ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalissar Dattawa.

Sanatan mai shekaru 66 a duniya, ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Ilimi sannan kuma ya yi gwamnan Kano na tsawon wa’adi biyu.

Ya kasance cikin waɗanda suka nemi shugabancin Najeriya a shekarar 2011.

Comments
Loading...