
A ranar Laraba 19, ga watan Janairun shekarar 2022, Dan-majalissar Dattawa mai wakiltar Mazabar Majalissar Dattawa ta Jigawa ta Gabas, Ibrahim Hassan Hadejia ya kaddamar da shiri na musamman domin saukakawa yara mata zuwa makarantu daga gidajensu, shiri irinsa na farko a Najeriya.
Shirin an masa take da Edukeke, wanda a atakaice ke nufi da temakawa harkar neman ilimi ta hanyar raba kekuna ga yara mata, masu karatu musamman na yankunan karkara wadanda ke yin tafiya mai nisa kafin su isa makarantunsu.
An fito da shirin ne domin yayewa yaran matsalolin da suke sha a hanyarsu ta zuwa makarantu, wanda a wani lokacin a kan samu masu debe kimanin kilomita 13 kafin su isa makarantunsu.
A kokarin Sanatan na gano matsalolin da suke hana wasu yaran zuwa makarantu musamman mata, ya gano cewa akwai karancin samun cigaban karatun yaran zuwa karamar sikandire, inda kusan kashi 40 cikin 100 suke kasa dorawa zuwa karamar sikandiren bayan kammala karatun firamare.

Akwai kwamiti na musamman da aka sanya domin bin diddigin lamarin, wanda a cikin zangon karatu daya ya samu nasarar binciken makarantu 70 wadanda dalibai daga kauyuka 171 ke zuwa neman karatu cikinsu.
Hadin-guiwa da hukumomin ilimi na kananan hukumomi, da shugabannin makarantu, kwamitin ya fitar da ka’idar cewa za a baiwa wadanda suke debe kilomita a kalla uku kekunan domin saukaka musu zuwa makarantun.
A kan haka, a karon farko an ware yara mata 100 sannan kuma ta hanyar amfani da ka’idoji na yawan zuwa makaranta da kuma kokarin karatu a karon farko an ware dalibai mata 720 wadanda ke debe tsakanin kilomita 5 zuwa 13 a kan hanyarsu ta zuwa makarantun.
Duk wadannan da aka ware sun mori wannan shiri, inda suka samu kekunan da za su na hawa zuwa makarantansu, baya da haka, a cikin shirin an samar da kekuna na zamani masu inganci ga duk dalibai masu bukata ta musamman.
Shirin Edukake na Sanata Ibrahim Hassan abu ne da zai cigaba, an tsara gudanuwarsa kan Bicycle Bank (Asusun Samar da Kekuna), wanda kungiyoyi da daidaikun mutane za su na tallafawa wajen sanya gudunmawar da za ai amfani da ita wajen samar da wasu kekunan.
Haka kuma shirin zai bibiyi nasarorinsa ta hanyar bincikar irin hazakar da yaran da suka mori shirin suke nunawa a makarantunsu, sannan kuma wadannan bayanai na yaran za a iya mika su ga masu bayar da gudunmawa idan sun bukata, domin kara samarwa yaran wadansu damarmakin na cigaban karatunsu.
A dai cikin shirin na Edukeke, suma malamai masu duba makarantun ba a barsu a baya ba, inda akaiwa masu kwazon cikinsu, wadanda za a tantance ta hanyar yawan zuwansu makarantun duba daliban (inspection) tanadin baburan hawan da za su yi amfani da su wajen aiyukansu da sauran bukatunsu na yau da kullum.

Haka kuma bayanan wadanda sukai kwazon daga cikin daliban da kuma malamai masu duba su, wadanda suka shafi kwazon malaman masu duba daliban da kuma kwazon daliban da suka mori shirin, za a mika su zuwa ofishin Sanata Ibrahim Hassan Hadejia da ke garin Hadejia.
Baya da batun kaddamar da rabon kekuna da babura, Sanata Ibrahim Hassan ya kuma kaddamar da gasar da za a na gudanarwa duk bayan watanni uku wadda akaiwa take da Best Brains, inda a karon farko za a raba manyan firizai, kekunan dinki da kuma babura, da nufin amfanuwar iyaye mata wadanda ake son su kara azama wajen bunkasa kokarin ‘ya’yansu.
Baya da haka kuma, za a ware wadanda sukai fice a cikin malamai, shugabannin makarantu, sakatarorin ilimi, da kuma shugabannin shiyya domin ba su kyauta ta musamman da nufin yaba musu da kuma karfafa musu guiwa.