For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaba Buhari Ya Ba Da Umarnin Kera Makamai A Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya ce, an baiwa Ma’aikatar Tsaro ta Najeriya umarnin kirkirar tsararriyar masana’anta ta sojoji domin kera makaman da za su cike gibin makaman da jami’an tsaron Najeriya ke bukata.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja a lokacin bude taron tattantance kokarin ma’aikatun gwamnatinsa wanda aka shirya domin sanin irin cigaban da ake samu wajen cimma manyan kudire-kudiren gwamnatinsa guda 9.

Buhari ya ce, kirkirar makerar ta sojoji zai rage yawan dogaro da Najeriya ke yi a kan wasu kasashe wajen samun makamai kayan aikin jami’an tsaro.

Ya ce shirin samar da makaman za a gudanar da shi karkashin Hukumar Kula da Kamfanonin Tsaro na Najeriya (Defence Industries Corporation of Nigeria (DICON), wani sashi na sojoji da ke da alhakin kula da kera makamai.

Comments
Loading...