A yau Laraba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin manyan sakatarori shida kafin fara zaman Majalissar Zartarwa na yau.
A watan Maris da ya gabata ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin manyan sakatarorin.
Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan ce ta sanar da amincewar Shugaban Kasar kan mutane shidan da suka tsallake tantancewar da ofishinta ya shirya a baya.
Da yake karanta bayanan manyan sakatarorin, Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Kafafen Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Femi Adesina ya ce, rantsuwar ta biyo bayan tantancewat makonni da a kai a kan manyan sakatarorin.
Wadanda aka rantsar din sun hada da Mahmud Kambari daga Jihar Borno, Esuabana Nko-Asanye daga Jihar Cross River, Adamu Lamuwa daga Jihar Gombe, Yakubu Kofarmata daga Jihar Kano, Olufemi Oloruntola daga Jihar Ogun da kuma Richard Pheelangwah daga Jihar Taraba.
NAN