For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Dawo Da Dukkan Ambasadojin Najeriya Gida

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo dukkan ambasadojin Najeriya da ke ƙasashe daban-daban gida, in ji Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje.

Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimakawa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Yaɗa Labarai na Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Amb. Yusuf Tuggar ya fitar.

KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Sa Jami’an Tsaro Su Ƙwato Bashin Da Aka Bai Wa Manoma Kafin Nan Da 18 Ga Satumba

Sanarwar ta ce, biyo bayan tambayoyi da ake ta yi kan dawo da ambasadan Najeriya a Birtaniya, Minsitan Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar na tabbatar da cewar, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo da dukkan ambasadojin Najeriya gida.

Sanarwar ta kuma ce, ambasadojin Najeriya da ke ƙasashe na zama wakilan ƙasa ƙarƙashin shugaban ƙasa, kuma damar shugaban ne ya tura su ko kuma ya dawo da su gida.

Tun da farko dai, Shugaba Tinubu ya dawo da Ambasadan Najeriya a Birtaniya, Sarafa Tunji Ishola wanda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a watan Janairu na shekarar 2021.

Comments
Loading...