For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban America Ya Nada Musulma Ta Farko A Matsayin Alkaliyar Kotun Tarayya

Shugaban Kasar America, Joe Biden, a karon farko ya nada mace Musulma ‘yar America a matsayin alkaliyar kotun gwamnatin tarayya a America, kamar yanda Fadar White House ta bayyana a ranar Larabar da ta gabata.

Idan har Majalissar Dattawan America ta aminta da nadin Nusrat Jahan Choudhury, lauyar kare hakkin al’umma ‘yar asalin kasar Bangladesh, to za tai aiki a kotun gwamnatin tarayya ta yankin jihar New York.

“An zabo wadda za ta zama ta farko ‘yar America mai tushe daga Bangladesh kuma ta farko ‘yar America Musulma ta zama alkaliyar kotun tarayya,” in ji Fadar White House a ranar Laraba yayin magana kan Nusrat.

Nusrat ta yi aiki a matsayin daraktar shari’a ta American Civil Liberties Union (ACLU), a yankin Illinois.

Ta kuma yi aiki a baya a matakai daban-daban a kungiyar, ciki har da mataimakiyar darakta ta ACLU bangaren shirin kula da nuna banbancin kabila a New York.

Ta kuma shiga cikin yunkurin kare hakkokin al’umma da dama, ciki har da wanda aka shigar da ‘yansanda New York kan zargin leken asiri kan Musulman birnin.

Comments
Loading...